‘Yan siyasa ke ruruta wutar rikicin kabilanci –Inji Sultan

0

Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar, ya dora alhakin ruruwar rikicin kabilanci a kan ‘yan siyasa, domin cimma biyan bukatun su ta hanyar haifar da rikice-rikice a kasar nan.

Sultan ya yi wannan ikirarin ne babban dakin ibadar Kiristoci a Saint David’s Cathedral da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Jiya Lahadi ne ya yi jawabin, a wurin taron kwanaki biyu da Cibiyar Tuntuba Tsakanin Addinai (NIREC), ta shirya.

Abubakar ya shawararci ‘yan Najeriya sun kaurace wa ‘yan siyasa da masu hannu da huni da ke tsoma rigar siyasa a harkokin addini.

Ya ci gaba da yin nuni da cewa Alkur’ani da Bebul ba su da alaka da kowace jam’iyya.

Dangane da zargin rushe masallaci da aka ce an yi Fatakwal, da aka zargi gwamnatin jihar Rivers da yi, ya ce tuni NIREC a matsayin ta uwa a kasa ta dauki hannun kamo bakin zaren, domin daidaita matsaya da samo maslaha.

Babban Basaraken Akure, wato Deji na Akure, AAladetoyinbo Aladelusi ne gayyaci Sultan domin halartar taron da ake gudanarwa a kowace shekara don inganta al’adu.

Ya kara da cewa mutum ko Musulmi ne shi ko Kirista, babu wanda zai fito ya na bobotai ko bugun kirjin wai shi ya na son Allah, ba tare da ya na so da kaunar makwaucin sa ba.

Aladetoyinbo a na sa jawabi kuwa, ya ce wannan biki an shirya shi ne domin inganta kusanci tsakanin mabiya addinai daban-daban a Jihar Ondo.

Manya da dama suka halarci taron, ciki har da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Jihar Ondo da kuma Shugaban Kungiyar Limaman Jihar Ondo.

Kafin sannan sai da Sultan ya bude sabon babban masallacin da aka gina a Fadar Deji na Akure din.

Share.

game da Author