Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta fitar da sanarwar shan alwashin kara tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna birnin.
Wannan sanarwa ta fito ne a daidai lokacin da ake ta watsa bayanan garkuwa da mutane da aka yi a ranar Asabar har a wurare shida daban-daban.
Amma kuma ‘yan sandan sun bayyana cewa an sako daya daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su, sauran kuma ana ta kokarin a ga an sake su.
Cikin sanarwar, jami’an tsaron sun bayyana cewa an sako malamin Jami’ar Baze da aka yi garkuwa da shi, kuma ana kokarin sako sauran.
Daga nan sai suka kara tabbatar wa mazauna birnin cewa Abuja lafiya kalau ta ke, kuma ‘yan sanda na ci gaba da kara bijiro da dabarun dakile duk wasu mugayen iri domin tabbatar da tsaron rayuka, lafiya da dukiyoyin jama’a.
Yayin da suka ce su na kokarin ceto wata yarinya da aka yi garkuwa da ita, aka gudu da ita, PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa yarinyar ‘yar tsohon dan takarar gwamnan jihar Adamawa ce, Umar Ardo.
Ya yi bayanin sace ta a kofar wani kantin zamani a Asokoro da dare, a shafin sa na Facebook, a ranar Asabar, sannan kuma a jiya Lahadi da dare an yi sanarwar karbo ta bayan an biya masu garkuwar diyyar dalar Amurka 15,000.
An sanar da cewa bayan an biya kudin, yarinyar ce ta buga waya ta ce a zo a dauke ta a Layin 4th Avenue a Gwarimpa.