‘Yan sanda sun kamo wadanda suka yi garkuwa da dan majalisan Kaduna

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ‘yan sandan Puff-Adder sun kamo masu garkuwan da suka yi garkuwa da dan majalisan Kaduna Sulaiman Dabo da daliban jami’ar ABU da aka yi garkuwa da su a titin Kaduna-Abuja.

A takardar da rundunar ta fitar wanda kakakin rundunar Yakubu Sabo ya saka wa hannu ya ce tun bayan sakin wadanda aka yi garkuwa da zaratan ‘yan sanda na ‘ Operation Puff-Adder suka fantsama dazukan dake kewaye da kangimi domin kamo wadannan masu garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa ‘yan sandan sun dira wasu maboyan maharan dake Maigiginya da Gurguzu duk dake karamar hukumar Igabi inda suka kama wasu masu garkuwa da mutane sannan suka kashe wasu kuma suka kwato bindigogi kirar AK47.

Haka kuma wani gogarman masu garkuwa da aka kama mai suna Buhari Bello wanda shine ya tona asirin sauran masu garkuwan da aka cafko a dajin Kangimi, ya ce kungiyarsu ya hada da masu garkuwan da ke aika-aika a Titin Kaduna-Abuja.

An samu Buhari da kullin kudi har naira 450,000 da ya ce wai rabon sa ne da aka bashi bayan an raba kudin fansa.

Kwamishinan yan sandan Kaduna yayi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da taimakawa ‘yan sandan juhar Kaduna da bayannan da zai sa a bankado maboyan wadannan ‘yan ta’adda.

Share.

game da Author