Duk da kashe ‘yan Najeriya da ‘yan wasu kasashe da ‘yan kasar Afrika Ta Kudu ke yi da hakan yasa yankin Afrika ta dau zafi a wannan kwanaki, bai hana wasu ‘yan Najeriya kwadayin zuwa wannan kasa ba.
Daya daga cikin manyan ‘yan Najeriya da ake ganin sune zasu fito su nuna bacin ransu karar game da abinda ake yi wa Najeriya sai gashi a yanzu haka ma suna can suna shan jammiya.
Kowa ya san yadda tsohuwar ministan Ilimin a lokacin mulkin Obasanjo, Oby Ezekwesili take nuna adawar ta kakara game da duk wani abu da take ganin take hakkin dan Adam ne sannan da irin rawar ta da take na kira da a sako ‘yan matan Chibok da Boko Haram suka yi garkuwa da amma sai gashi a wannan karon ita ce kan gaba wajen zuwa kasar Afrika ta Kudu domin halartar Taro.
Idan ba a manta ba hatta mahukunta a Najeriya sun janye daga halartar taro WEF da ake yi a kasar saboda cin mutuncin ‘yan Najeriya da ake yi a kasar.
‘Yan Najeriya gaba daya kaf sun nuna fushin su karara a dalilin halartar wannan taro da Oby tayi a kasar Afrika Ta Kudu din.
” Idan akwai mutum daya da ban zan taba yadda cewa za ta halarci wannan taro ba, ba zai wuce Oby ba amma sai gashi ta tafi kasar da basu kaunar mu, ba su kaunar ‘yan Najeriya.
” Duk da irin cin mutunci da zarafin ‘yan Najeriya da ake yi a kasar Afrika Ta kudu, mawaka ma da dama sun soke wasanni da zasu yi a kasar, sai gashi irin su Oby ne za su tafi kasar domin halarta wani taro. A gaskiya ta zama bakin ganga.
Sai da kuma ita Oby tace ta halarci taron ne domin ta tuna wa mahukuntan kasar Afrika Ta Kudu cewa lallai fa hari da mutanen su ke kai wa baki a kasar ba abu ne da za su bari ana ci gaba da yi ba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wa jakadan Najeriya a Kasar Afrika Ta kudu kiranye da ya dawo Najeriya sannan ya aika da tawaga ta musamman domin ganawa da mahukunta a kasar.
Discussion about this post