Jakadar Najeriya Burkina Faso, Ramatu Ahmed, ta bayyana cewa akalla kananan ‘yan mata ‘yan Najeriya da ke karuwanci a kasar Burkina Faso ba za su kasa kai su 10,000 ba.
Ramatu ta bayyana wannan abin takaicin ga wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Wagadugu, babban birnin kasar.
Ta bayyana cewa dukkan su da ke wannan sana’a ta karuwanci, su na rayuwa ne a cikin wani mummunan hali a sansanonin masu hakar ma’adinai da ke kasar.
Ramatu wadda aka tura jakadanci kasar tun cikin watan Agusta, 2017, ta ce sama da ‘yan mata 200 suka amince aka maido su gida Najeriya.
Sannan kuma ta kara da cewa yawancin matan wadanda aka yi wa alkawari da romon-baka da romon-kunne ne aka rabo su daga Najeriya da nufin za a kai su kasashen Turai domin a samar musu ayyuka a can.
“Yawan wadannan mata da aka rabo su da Najeriya suke karuwanci a kasar nan, abin damuwa ne sosai ga Najeriya. Akwai akalla su 10,000.
“Akasarin wadannan ‘yan mata kuma duk masu kananan shekaru ne; sun bar makaranta, su na nan su na ta tambele, gallafiri da karuwanci a Burkina Faso.
“Baya ga cewa wannan abin takaici ya na zubar wa Najeriya da kima da martaba, kuma abin damuwa ne matuka, musamman idan aka yi la’akari da lafiayar su.
“Yawanci wadanda ke so su koma gida, su na son komawa ne, saboda tun farko dama ribbatar su aka yi, aka rabo su da gida, ba su san za su tsinci kan su a halin karuwanci a nan kasar ba.
“Kaicon shi ne, duk inda ka ci karo da yarinya daya tal ta nuna maka ta na son komawa gida Najeriya, to kuma za ka samu wasu goma a cikin dazuka wadanda zuciyoyin su sun bushe, ba su son komawa gida, sun kama zaman-dirshan a nan Burkina Faso.” Inji Jakada Ramatu.
Daga nan sai ta yi tir da ‘yan Najeriya masu safarar wadannan matan daga Najeriya su na hure musu kunne. Ta ce ofishin ta zai ci gaba da kokarin gano su tare da hadin kan jami’an tsaro na cikin karkarar kasa domin a hukunta su.
Ofishin ta kuma na kokarin hadin kai da Hukumar Kula Da Fatauci da Safarar Jama’a domin maida wadanda ke son komawa gida.
Wannan hukuma ta kuma fara korafin cewa kudaden da ake ware mata duk su na tafiya ne wajen kwasar ‘yan Najeriya a kasashen Afrika ta Yamma ana maida su gida. Daga nan hukumar ta kara da cewa nan gaba kadan ba za ta iya daukar wannan nauyin ba.
Daga nan sai Ramatu ta yi kira ga iyayen yara mata a Najeriya da su rika kula da ‘ya’ayan su.
“Wasu matan sun ce mana iyayen su ba su san sun fito daga Najeriya ba. Wasu kuma iyayen su sun sani, wasu uban su ya turo su, wasu kuma uwar su. Wasu ma iyayen su ko kawunnan su ne suka turo su.
Idan ba a manta ba, a wani rahoto da PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cikin 2018, Darakta-Janar na Yaki da Fataucin Yara Mata. Julie Donlie ta bayyana cewa akwai mata ‘yan Najeriya kimanin 20,000 da ke karuwanci a sansanonin hako ma’adinai a kasar Mali.