Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 18, wadanda dukkan su fasinjoji ne da ke cikin wata mota bas.
An yi garkuwa da su a kan hanyar Otan Ile/Imesi cikin Jihar Osun.
Rahotanni sun kuma kara tabbatar da cewa daya daga cikin masu garkuwan ne ya yi basaja a cikin motar, wanda aka dauki shi a matsayin fasinja.
Wadanda tsautsayin ya ritsa da su dai matafiya ne daga Osogbo, kan hanyar su ta zuwa Abuja.
An tare su tare da yin garkuwa da su a daidai mahadar Ajeoku, kan babban titin Otanle/Imesile a jiya Lahadi da dare.
An tasa keyar dukkan fasinjojin zuwa cikin surkukin daji, kuma har ya zuwa yau Litinin da rana, masu garkuwan bas u tuntubi ko daya daga cikin iyalan wadanda suka yi garkuwar da su ba.
Kakakin ’Yan Sanda ta Jihar Osun, Folashadi Odoro, ta bayyana cewa tabbatar an yi garkuwa da mutanen. Amma kuma ta ce ba a tabbatar da ko mutane nawa ne aka yi garkuwa din da su ba.
“A halin yanzu ba za mu iya cewa ga adadin yawan fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba. Amma dai ina tabbatar da cewa mu na bakin kokarin ganin mun kubutar da su.” Inji Odoro.
Daga baya kuma ta sanar cewa an saki hudu daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su.
Daga nan ta ja hankalin jama’a tare da yin kira su rika kai rahoton duk wani bakon-idon da ba su amince ko sakankance da shi ba.