Yadda Boko Haram suka kwace kudaden alawus din sojoji 20,000

0

Boko Haram sun yi wa jerin-gwanon tawagar sojijin Najeriya kwanton-bauna, har suka kwace kayan yaki tare da makudan kudade.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an kai wannan harin ne a ranar Juma’a da misalin karfe 9 na safe, tsakanin dajin Azare zuwa Kamuya, kan hanyar zuwa Damaturu.

An gwabza gumurzu tsakanin ‘yan ta’adda da sojojin Najeriya, zaratan musamman na 3 da na Bataliya ta 231 da ke karkashin ‘Operation Lafiya Dole’.

Boko Haram sun yi wa sojojin kwanton-bauna a lokacin da suka shiga hanya mai ramuka da kwazazzabai, inda suka jikkata soja daya kuma suka arce da motar yaki daya.

Majiya ta kara tabbatar da cewa motar yakin da aka kwace ta Bataliya ta 231 ce, kuma an tsere da tsabar kudi har naira milyan 15, 492, 00.

Kudaden dai an tabbatar wa jaridar mu cewa kidaden alawus ne na kwanan-daji a ke bai wa sojoji naira dubu daya kullum, da aka dauko domin biyan sojoji su dubu 20 kudin kwanan-dajin sati daya.

An tura sojojin agajin gaggawa daga Damaturu, inda suka kashe Boko Haram daya.

Share.

game da Author