Hukumar NDLEA na jihar Adamawa ta bayyana cewa a cikin makonni uku da suka gabata hukumar ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 25 da kilogram 166.95 na miyagun kwayoyi a bangarori daban daban na jihar.
Shugaban hukumar Yakubu Kibo ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Yola.
Kibo ya bayyana cewa a ranar biyar ga watan Satumba hukumar ta kama wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Mohammed Kawuwa mai shekaru 59 da daurin ganyen wiwi da ya kai giram 600 a Jimeta-Yola.
Kuma a ranar tara ga watan Satumba hukumar ta kama kwalaben magungunan tari da ake kira kodin guda 218 da kwayoyin maganin Rohypnol da ya kai giram 350 a Mubi.
Sannan kuma a garin Gombi hukumar ta kama babbar mota dankare da kwayoyin Tramadol da ya kai kilogram 107 da wasu kwayoyi sannan ta kama mutane biyu da ke da hannu a safarar wadannan kwayoyi.
Bayan haka hukumar ta kama Yusuf Mohammed da ganyen wiwi da ya kai kilogram 10.2.
Mohammed ya bayyana cewa ya shuka ganyen ne a gidansa dake karamar karamar hukumar Jada.
Kibo yace sun kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi biyu, Abdulrasheed Mohammed da Mohammed Ali da kilogram 10 na maganin allurar Pentazocine da kilogram 3.8 na wiwi.
An kuma kama Lawal Abdullahi,Sulaiman Waziri da Nura Musa dake da hannu a aikata wannan ta’asa.
Kibo yace hukumar ta kama wadannan masu safarar miyagun kwayoyin ne da maganin Diazepam kilogram 168,katan-katan din allurar maganin Pentazocine da tabar wiwi dauri-dauri bann daban.
Ya ce da zaran hukumar ta kammala bincike za ta mika su ga hukuma.