A karo na biyu jirgin Air Peace ya sake dauko wasu karin ’yan Najeriya 319 daga Afrika ta Kudu, ya maido su Najeriya.
An sauke su a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Lagos, daidai karfe 7:21 na dare.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najieriya ta bayyana komai dangane da wadanda jirgin ya dawo da su.
Kafin wadannan 319 dai an fara maido wasu 178, kuma dukkan su sun dawo ne don radin kan su. Su din na farkon ma Air Peace ne ya dauko su.
Kafin isowar jirgin dai sai da Majalisar Tarayya ta gayyaci shugaban kamfanin jiragen Air Peace, Allen Onyema, inda ta gode masa tare da jinjina masa irin aikin jinkai tare da kishin Najeriya da ya nuna, wajen dauko ‘yan Najeriya kyauta daga Afrika ta Kudu.
Shugaban Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa tilas a yaba wa Onyema, domin ya sadaukar da ainihin harkar sa ta kasuwanci, ya maida jirgin sa abin dauko jama’a kyauta ba tare da biyan ko sisi ba.
An gayyaci Onyema ne an yi masa wannan jinjina a lokacin da zauren majalisa ke cike makil.
Daga nan sai Gbaja ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bai wa Onyema lambar yabo ta girmamawar nuna kishin kasar sa da ya yi.
LEGAS TA BA KOWANEN SU AGAJIN NAIRA 20,000
Gwamnatin Jihar Lagos ta bai wa kowane dan Najeriya da aka dauko daga Afrika ta Kudu a jiya Laraba, agajin Naira 20,000.
Su 319 ne aka sauke a filin jirgin sama na Murtala Mohammed jiya Laraba da ke Legas.
An dawo da su ne mako daya bayan fara kwaso wasu 178 da aka fara daukowa, bayan kashe-kashen kin jinin bakar fata ‘yan Afrika ta yi kamari a Afrika ta Kudu.
Jirgin kamfanin Air Peace ne ke jigilar dawo da su gida Najeriya kyauta.
Air Peace kirar B777 ne ya dauko tawagar da ta sauka jiya Laraba, su 319 a Legas. Bayan saukar ta su ce kuma gwamnatin jihar Legas ta bai wa kowanen su naira 20,000.
Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya da ke Kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ce tare da Allen Onyema, mai kamfanin Air Peace, tare da Mai Taimaka Wa Gwamnan Legas kan Ayyuka na Musamman, Jermaine Sanwo-Olu suka yi musu kyakkyawar tarba a filinn jirgin na Legas.