Wani ya rataye kan sa a Katsina

0

Wani mutum mai suna Badamasi Musa, ya kashe kan sa a garin Kabomo, cikin Karamar Hukumar Bakori, Jihar Katsina.

An samu gawar Badamasi, mai shekaru 35 da haihuwa rataye ta na lilo a jikin wata bishiya a bayan garin Kabomo. Wasu manoman da suka yi sammakon zuwa gona da safiyar yau Alhamis ne su ka ga gawar.

Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya kara da cewa an tabbatar Badamasi na fama da ciwon tabuwar kwakwarwa, wanda ake dangantawa da musabbabin rataye kan sa da ya yi.

“A yau wajen karfe 10 na dare wani mai suna Badamasi Musa mai kimanin shekaru 35 da haihuwa, ya rataye kan sa a bayan garin Kabomo. An san shi da matsalar tabin hankali. Ya kashe kan sa ta hanyar daura igiya a bishiya sannan ya rataye kan sa.

Daga nan ya kara da cewa an dauki gawar sa zuwa asibitin Bakori domin likitoci su yi bincike.

Amma kuma ya ce a gefe daya ana ci gaba da bincike domin a gano gaskiyar musabbabin kashe kan sa din da Badamasi Musa ya yi.

A ‘yan shekarun nan, ana ci gaba da samun rahotannin masu kashe kan su a garuruwa daban-daban a kasar nan.

A baya-bayan nan ma sai da hukuma ta haramta shigo da wani maganin kwari mai suna ‘Snipper’, wanda mutane da dama suka rika sha su na kashe kan su.

Share.

game da Author