Tattaunawar wadda PREMIUM TIMES ta yi da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, ta na da tsawo. Wannan kashi na daya ce.
PT: Ya ake ciki game da rahoton yadda zaben 2019 ya gudana?
MY: Da farko dai ku sani cewa mun yi alkawari ga daukacin ‘yan Najeriya cewa za mu bada cikakken rahoton yadda zaben 2019 ya gudana dalla-dalla. To mun fara tattara bayanai daki-daki tun daga matakin hukumar zabe zuwa jihohi da Abuja. Kusan zan iya ce muku rahoton ma ya kammala. Sannan kuma mun yi alkawarin yin amfani da dukkan darussan da mu ka koya a zaben 2019 wajen gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa, cikin watan Nuwamba mai zuwa.
Daga cikin darussan da mu ka koya a zaben 2019, shi ne muhimmancin fara shirye-shirye da wuri. To dalili mu ka kudiri cewa lallai kayan aikin zaben gwamna a Bayelsa sa Kogi sun zo hannu tun cikin watan Agusta, akalla watanni biyu da rabi kafin zaben kenan.
Daga nan kuma sai barun raba kayan zabe. Za mu fara rabawa da wuri, kuma mun tabbatar kayan zabe sun Isa inda lunguna da sakon duk da suka kamata a kai su.
Sai kuma batun na’urar tantance masu dangwala kuri’a. A kan wannan batu ma za mu bijiro da sabbin hikimomin saukaka irin sarkakiyar da aka samu a zaben 2019.
Dangane da zanen Bayelsa da Kogi, akwai akalla katin jefa kuri’a 50,000 da masu su ba su karba ba a Bayelsa. Akwai 17,000 da har yau ba a karba ba a Kogi.
Saboda haka za mu sanarwar kowa ya je ya karbi nasa. Kuma za mu lika sunayen duk wanda bai karbi nasa ba. Sannan kuma za mu bi lambobin wayar su duk mu tura musu sakonnin cewa su je su karbi katin su. Sannan kuma za mu fito da lambobin da za a kira domin wanda ya daburce sai ya kira domin ya ji a inda zai je ya karbi na sa katin.
Za mu dauki ma’aikatan zabe 9,000 a Jihar Bayelsa, 15,000 a Jihar Kogi. Za mu ba su horo da wuri. Game da jami’an tsaro kuwa, tuni har mun rubuta wa Sufeto Janar na ‘yan sanda bukatar jami’an da za su sa-ido a harkar zaben.
Sannan kuma za mu damka wa dukkan jam’iyyun da suka shiga takara sunayen wadanda suka yi rajista, kwanaki 30 kafin ranar zabe.
PT: Ba ka ganin akwai bukatar buga wadannan sunaye a shafin INEC na intanet yadda kowa zai gani?
Yakubu: Abin da doka ta ce mana shi ne mu aika wa dukkan jam’iyyun da suka shiga takara aunaywen kawai. Amma kada ku manta, kafin zaben 2019, mun dukkan mazabu mun lika sunayen wadanda suka yi rajista don wanda bai ha sunan sa ba ya sanar, ko kuma wani korafin daban.
Amma za mu duba wannan batu na buga sunayen a shafin INEC na Intanet da ku ka bijiro da shi.
BATUN SAKE YIN RIJISTA GA WANDA BAI YI BA
INEC ba za ta ci gaba da sake yi wa wadanda ba su da rajista sabon kati ba. Saboda babu lokaci idan aka yi la’akari da yadda zaben Bayelsa da Kogi ya zo bayan zaben 2019. Amma dai za a iya ci gaba a cikin sabuwar shekara.
PT: Amma dai mun san ka ji haushi ganin yadda ba a sa wa kudirin sabuwar dokar zabe hannu ta zama doka kafin zaben 2019 da ya wuce ba. Shin haka ya daburta maka aiki ko saukakawa ya yi?
Yakubu: Ai abubuwa da dama sun sha mana kai kuma sun daukar mana hankali mu na ta gaganiyar aikin zabe a lokacin. Ba mu da lokacin tsayawa nuna damuwa kan abin da ba mu iya yin komai a kai.
Aikin gyaran dokar zabe ya rataya ne a wuyan bangaren zartaswa da kuma majalisar tarayya. Amma dai mun so a ce sun kammala komai da wuri.
BATUN KUDADEN DA JAM’IYYU KE KASHEWA LOKACIN KAMFEN
PT: Dokar INEC ta jaddada cewa tilas jam’iyyun da suka shiga takara su kai wa INEC rahoton kudaden da suka kashe a lokacin kamfen da sauran su. Zuwa yanzu jam’iyya nawa ce ta kawo wa INEC na ta rahoton?
Yakubu: To ita dai doka ta ce kowace jam’iyya ta kawo wa INEC dalla-dallar adadin kudaden da ta kashe. Domin akwai adadin da doka ta shar’anta jam’iyya ta kashe wajen gudanar da ayyukan ta da kuma wajen kamfen. Amma dokar cewa ya yi su kawo cikin watanni shida bayan zabe.
Duk da dai ma san watanni shida din ba su kai ga cika ba, amma wasu jam’iyyu kalilan sun kawo na su rahoton. Za mu tashi mu sake tunatar da saura da su hanzarta aiko na su rahoton kafin wa’adin watanni shida ya cika.
Discussion about this post