SULHUN ZAMFARA: ’Yan bindiga sun saki jimillar mutane 372 – Kwamishinan ‘Yan Sanda

0

Sulhun da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi da ‘yan bindiga masu garkuwa da kai hare-hare, ya samu nasarar sakin mutane 372 da aka yi garkuwa da su.

Haka kuma an samu adadin ‘yan bindiga 240 wadanda suka mika makaman su tare da tuba daga aikata mugayen halaye.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, Usman Nagogo ne ya bayyana haka.

Nagogo wanda shi ne Shugaban Shirin Sulhun Zaman Lafiya a Jihar Zamfara, ya yi wannan bayani ne jiya Lahadi a wani taro a Bakura, wurin ci gaba da irin tarukan samar da zaman lafiya da tattauna fahimtar juna da ake ci gaba da gudanarwa.

Sannan kuma ya yi karin haske cewa maharan da ake addabar wasu jihohi a kasar nan ba wai Fulani zalla ba ne.

“Akwai wasu kabilu da yawa a cikin mahara. Ba Fulani kadai ba ne ke yin Garkuwa da mutane.”

Daga nan sai ya zargi ‘yan banga da laifin ruruta wutar rikicin fadan makiyaya da manoma, wanda ya haifar da barkewar ‘yan bindiga sun a kashe-kashe da kone-kone da garkuwa da mutane.

Ya ce ‘yan banga ko ‘yan sintiri sun rika kashe wasu da suke kamawa ba tare da damka su a hannun hukuma ba.

Ya ce wasu hare-hare da aka rika kaiwa, duk ramuwar gayya ce daga kisan da ‘yan sintiri suka rika yi, ba tare da kwakkwaran binciken wanda aka kashen mai laifi ne ko bai aikata ba.

Daga nan sai ya nuna gamsuwa da irin nasara da ci gaban da aka rika samu tun bayan kwafa kwamitin sasanta zaman lafiya a jihar.

“A can baya an daina cin kasuwannin wasu garuruwa saboda matsalar tsaro. Amma a yau an bude kasuwanni, Fulani kuma su na karakainar su, ba tare da tsangwamna ba.

“Da irin wannan ci gaba, zan iya cewa an ci gagarimar nasara sama da kashi 90 bisa 100.”

Daga nan ya roki jama’a su goya wa wannan gagarimin shirin samar da dawwamammen zaman lafiya a Jihar Zamfara.

Share.

game da Author