‘Yan Najeriya musamman shugabanni da mazauna kowacce kusurwa na kasarnan sun nuna bacin ransu matuka ga mahukuntar kasar Afrika ta kudu ganin yadda ‘yan kasar da ba tun yau ba suke bin ‘yan Najeriya suna bugewa kawai wai don suna zaune a kasar su.
Abin da yake faruwa a ‘yan kwanakinnan a kasar ya tada wa mutanen Najeriya da dama hankali ganin cewa Najeriya na daga cikin kasashen da suka rika taimakawa kasar a lokacin da turawa ke yi mata mulkin danniya ko kuma kama-karya.
Najeriya ta jajirce matuka wajen ganin ta tallafawa kasar Afrika ta kudu da duk irin taimakon da take bukata a wannan lokaci amma sai gashi yanzu basu da makiya irin ‘yan Najeriya a Duniya.
Baya ga wannan gata da suka samu daga kasa Najeriya, kamfanonin kasar sun mamaye Najeriya suna cin karen su ba babbaka amma duk a banza, a duk lokacin da suka bukaci su farwa ‘yan Najeriya sai su farmusu sun bibbigewa.
‘Yan kasuwa mazauna kasar basu tsira daga wadannan hare-hare ba. Mutum kawai zai wayi gari ne yaga matasa sun tunkari shagonsa suna kwashe kayan ciki sannan su lakada masa dukan tsiya idan ya nemi ya hana su sannan su biya gidaje suna bugewa kamar kaji.
Babban dalili kuwa shi wai ‘Yan Najeriya sun zo kasar su suna kwace musu ayyuka. Sannan kuma wai matan su sun fi son yin harka da ‘yan Najeriya fiye da su ‘yan kasan.
A dalilin abinda ya faru a ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya sun fusata matuka musamman a jihohin Kudu inda tuni suka fantsama manyan tituna suna cinna wa tayoyi wuta domin nuna fushinsu ga yadda ake kashe ‘yan Najeriya a kasar Afrika Ta Kudu din.
A ranar Talata dai an rika bi ana kokarin ciccinna wa ofisoshin MTN da Shagunnan Shoprite wadanda mallaki ‘yan kasar Afrika ta Kudu ne. Sannan wasu sun farwa ofishin Talabijin na Multichoice masu mallakin DSTV a jihar Legas. Nan ma sai da jami’an tsaro suka kawo dauki.
Ya zama dole a ja wa mahukuntan kasar Afrika Ta kudu da su rika ja wa mutanen kasar su kunne su daina cin zarafin baki dake zaune a kasarsu. Domin kasashe da dama basu samu goyon bayan da suka samu a lokacin da suke wahala ba, musammam irin wanda Kasa Najeriya ta rika yi wa kasar Afrika ta kudu din.