Shehu Sani ba shi da takardun cancantar da za a iya daukar sa aikin gwamnati a Kaduna – EL-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya shiga shafin sa na Twitter, inda ya gwasale tsohon sanata Shehu Sani cewa mai yiwuwa ma ba shi da cancantar da za a iya daukar sa aikin gwamnati a Jihar Kaduna.

El-Rufai da Shehu Sani a baya duk ‘yan jam’iyyar APC ne, amma daga baya Sani ya koma PRP a zaben 2019.

Ya fadi zabe inda dan takarar da El-Rufai ya tsayar, Uba Sani ya kayar da shi.

“Babu tabbacin ko ya cancanci ma a iya daukar sa aiki a Hukumar Daukar Ma’aikata ta Jihar Kaduna!”

Haka El-Rufai ya rubuta a shafin sa na Twitter din sa mai suna @elrufai, a yau Juma’a, karfe 9:35 na safe.

Daga nan kuma ya lika alamomin dariya a karshen rubutun.

Sai dai kuma bakar magana a cikin rasher da El-Rufai ya yi wa Sanata Sani, ramuwar gayya ce, domin sanatan ne ya fara shiga na sa shafin Twitter din ya caccaki tsarin fara biyan mafi kankantar albashi da Jihar Kaduna ta bayyana za ta fara daga biyan albashin watan Satumba da mu ke ciki.

“Duk wani biyan mafi kankantar albashi da kowace jiha za ta yi, wanda ba a bisa tsarin da sabuwar dokar biyan albashi ya ke ba, to yaudara ce kuma harkalla ce. Sannan kuma cuta ce. Duk mai son jin yadda tsarin biyan sabon albashi ya ke, ya fara tuntubar Kungiyoyin Kwadago tukunna, ba wai ‘yan siyasa ba.”

Abin da Sanata Sani kenan ya fada jiya Alhamis a shafin sa na Twitter.

El-Rufa’i da Sani sun dade su na adawa. Ko farkon wannan makon da El-Rufai ya shigar da dan sa makarantar gwamnati a Kaduna, sai da Sanatan ya gwasale shi, ya ce duk karya da burga da hauragiyar neman wurin zama ne a siyasar 2023.

“Mazauna Kaduna dai sun san yadda makarantun gwamnati su ke a yanzu a Kaduna. Sun san inda su ke, kuma sun san yadda kamannun su ya ke. Sun kuma san irin matsalolin da ke addabar su.” Haka ya shaida wa ‘yan jarida.

“Abin da ya yi na saka dan sa makarantar gwamnati kawai fa wasan kwaikwayo ne.

“Wasan kwaikwayo da aka rubuta labarin sa a birkice. Shirin Kannywood na ‘yan wasan Hausa ne, ko kuma Nollywood na ‘yan wasan Kudu. An shirya labarin ne domin kafafen yada labarai su yayata karkataccen shirin sa na 2023 kawai, ba wani abu ba.

“Ai kamata ya yi ya fara gyara dukkan makarantun Kaduna tukunna. Amma ya za ka kashe wa makarantar da za ka kai dan ka har naira milyan 195, kuma ka dauki ‘yan jarida su raka ka kai dan na ka makarantar, sannan har ka yi makahon tunani ko tinkahon cewa wai kai ka yi wani abin koyi? Ahaf!” Inji Sanata Sani.

Share.

game da Author