Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) da hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Bauchi (BSHCDA) ta bayyana cewa akalla mutane 23 ne suka rasu a dalilin kamuwa da zazzabin shawara a karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi.
A wata takarda da hukumar NCDC ta raba wa manema labarai cutar ta bullowa ne a karamar hukumar Alkaleri tun a ranar 29 ga watan Agusta sannan tun daga ranar 11 ga watan Satumba hukumar take gwada jinin mutanen jihar.
Hukumar ta ce ta yi wa mutane 169 gwajin jini tun daga wancan lokaci zuwa yanzu. Mutane biyar ne aka samu cikin wadanda aka yi wa gwajin na dauke da cutar.
Har yanzu dai hukumar na ci gaba da gwajin jinin mutanen jihar a hedikwatanta dake Abuja.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Hukumar BSHCDA ta bayyana cewa gwamnati za ta yi feshin magani a dajin Yankari domin hana yaduwar Zazzabin Shawara da sauran cututtuka a jihar Bauchi.
Gwamnati ta ce za ta yi amfani da jirgin sama wajen yin wannan feshin magani don kashe kwarin dake baza wannan cuta.