Ban ce har kudancin kasar nan ba, amma dai a Arewa kakaf jama’a da dama sun fi maida hankali a kan shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano, wadda jam’iyyar PDP ta shigar tare da dan takarar ta Abba Kabiru Yusuf.
Sun shigar a Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Gwamna, kuma an shafe lokaci ana musayar yawu tsakanin lauyoyin bangaren masu kara da kuma na wadanda ake kara, wato APC da INEC da kuma dan takarar APC, wato Gwamna Umar Ganduje da ke kan zango na biyu a yanzu haka. Kuma shi ne aka sanar ya yi nasara.
Hankulan jama’a da dama bai karkata a kan shari’ar zaben shugaban kasa ba, da aka tafka tsakanin Atiku Abubakar da Shugaba Muhammadu Buhari. Wasu na ganin ai da wahala Atiku ya kayar da Buhari, don haka ba su damu ba. Wasu kuma dama ba su ma gamsu da wasu hujjoji da Atikun ya rika tutiya da su ba, kamar ikirarin sa na bayyanar rumbun tattara alkaluman kuri’un zabe, wato ‘server.’
Jama’a sun maida hankali ne a ga yadda shari’ar Kano za ta kaya. Ko ba komai dai, a can baya kotu ta taba tsige gwamna bayan an yi zabe. Amma kuma ba ta taba tsige shugaban kasa ba.
Wani abin dubawa dangane da shari’un zabukan gwamna a zaben 2019 da aka gudanar, an kammala da dama daga cikin su, amma babu gwamna ko daya da Kotun Daukaka Kara ta tsige.
An kammala shari’ar zaben Gwamnan Jihar Katsina. Haka Taraba da sauran jihohi da yawa. Har yau kotu ba ta tsige gwamnan APC ko na PDP ba. Amma an tsige sanatoci, mambobin majalisar tarayya da na jihohi. Wasu da ba su hakura ba, sun garzaya a gaba. Wadanda kuma babu hurumin wucewa gaba, shikenan, sun tsigu.
Kafin a samu xi gaban zqmani a fannin likitoci, idan mace ta dauki ciki, babu yadda za a iya gane shin abin da za ta haifa din nan namiji ne ko mace? Da daya ne ko tagwaye?
Amma yanzu da ci gaba ya zo, likitoci na iya gane abin da mace za ta haifa, tun a farkon daukar cikin ta Ba sai an dauki tsawon watanni ba.
To sai dai kuma duk da irin wannan ci gaban zamani da aka samu, shari’ar zaben gwamnan Jihar Kano ta ‘gagari Kundila.’ Wato ba ka da mai iya ce maka ga yadda za ta karke. Ba lauya ba, ko likita ba zai iya auna cikin da kotun ke dauke da shi ya ce ga abin da ta za haifa ba.
Sai dai mu jira ranar haihuwa ta zo. Ranar da ko ma wa kotun ta haifa, rada masa suna dai mai yiwuwa sai a wata kotun ta gaba. Domin a ranar duk wanda aka ce cikin na sa ne, don haka dan ma na sa ne, to dayan da wahala ya amince. Sai ya yi jayayya.