Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Alhamdulillah, muna godiya ga Allah, mai kowa mai komai, mamallakin dukkan komai.
Alhamdulillah, ina da tabbacin cewa duk duniya ta saurari jawabin da Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya gabatar ranar laraba, 16/12/2015 a wurin gabatar da addu’ar zaman lafiya da aka saba gabatarwa a babban Masallacin Juma’ah na garin Kano, da ke jikin fadar Sarki; Sarkin Yayi bayanai masu matukar fa’idah akan rikicin ‘yan Shi’ah da jami’an tsaro na sojojin Najeriya.
A lokacin da Mai Martaba Sarki yayi wannan jawabi duk duniya ta saurari bayanan sa, da shawarwarin sa, domin ba a boye yayi su ba; kuma al’ummah, musamman mabiya Sunnar Annabi Muhammad (SAW), kuma masoya Sahabban Manzon Allah (SAW) da ahalin sa, sun jinjina masa akan wannan jarunta ta sa, da namijin kokarin sa wurin fadin gaskiya komai dacinta, kuma ko akan waye.
Wadannan jawabai na Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II muhimmai, masu kayatarwa, bayan kafafen yada labarai masu tarin yawa na gida da na waje da suka ruwaito su, hatta kafar yada labarai ta BBC Hausa sun ruwaito labarin ranar alhamis, 17/12/2019, domin muhimmancin su ga samar da zaman lafiya a cikin Al’ummah.
A cikin shawarwarin da ya bayar, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II yace bai kamata kungiyoyin addini su rika keta dokokin kasa ba, sannan ya kara da cewa kuma bai kamata hukumomi suyi amfani da karfin da ya wuce kima akan ‘yan kasa ba.
Duk wadannan shawarwarin ya bayar da su ne a wurin taron addu’o’i na musamman da ya jagoranta, a daidai lokacin da ake zaman zulumi, bayan kisan da sojojin kasar nan suka yi wa mabiya addinin shi’a, wadanda, a cewar su, sun yi yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, wato Janar Tukur Buratai.
Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II yace kamar yadda yake babu wata kungiyar addini da za ta mayar da kanta hukuma, su ma jami’an tsaro bai kamata su rika bude wuta a kan kowane irin laifi ba.
A cikin jawaban, Mai Martaba Sarkin ya bukaci kungiyoyin addinai da su zamo masu da’a, da kaucewa tada-zaune-tsaye da tsokano fitina saboda ba’a san karshen ta ba, sannan ita kuma gwamnati ta rika jan hankalin jami’an tsaro da su rika hakuri kadan, saboda a takaita salwantar rayuka.
Sannan Mai Martaba Sarki ya tabo tarihi, a inda yace, mu a kasar nan ba mu san zagin Sahabban Manzon Allah (SAW) ba. Sannan yace, duk wata akida da aka shigo da ita kasar nan ta zagin manyan abokan Annabi (SAW), wato Sahabbai, ba mu san ta ba, sannan ba mu gaje ta ba a wurin magabatan mu da suka yi jihadin tabbatar da wannan addini; irin su Shehu Dan Fodiyo da sauran su. Sarki yace, abun da muka sani, kuma muka gada daga magabata, shine bin Sunnar Annabi Muhammad (SAW).
Ya ku ‘yan uwa na Musulmi masu girma, masu daraja, masu albarka, shin anan ina hada ku da Allah; don Allah, don Allah, don Allah a cikin wadannan jawabai da bayanai da shawarwari na Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II akwai karya a ciki? Akwai kauce wa hanya a ciki? Akwai kin wasu mutane a ciki? Idan akwai, don Allah kar ku boye, ku fito kuyi bayani, domin mu har kullun, so muke yi a fito da gaskiya fili, kiri-kiri, domin kowa ya gane ta, kuma ya fahimce ta. Mu a cikin al’amarin mu babu nuku-nuku, kuma babu munafunci wallahi!

To kun ji fa, ya ku jama’ah, wai saboda wadannan maganganu da Mai Martaba Sarki yayi, shekaru sama da hudu a baya, maganganun da duk mai hankali, mai nufin Najeriya da alkhairi, da duk wani mai kaunar zaman lafiya, yasan cewa suna kan hanya, sai ga ‘yan shi’a yau sun zakulo su, bayan har an manta da su sun wuce, sun hada kai da makiya Mai Martaba, wai za su yake shi akan su. Yanzu haka suna nan suna ta yada kamfen na batanci, da sharri, da kazafi, da kage akan Sarki, ta kafafen yada labarai na zamani, da intanet; irin su Facebook, WhatsApp, Twitter, Instagram, Telegram da sauransu.
Suna nan suna ta rubuce-rubuce da yada hotunan karya, wadanda aka hada su ta hanyar hade-hade irin na kwamfuta, da nufin sharri. Wai don su rage wa Mai Martaba Sarki daraja a idon mutane. Amma ayyah, ba su san da cewa sun makara ba. Domin a lokacin da suke yada wannan sharri, a lokacin ne kuma Allah Subhanahu wa ta’ala cikin ikon sa, yake karawa Mai Martaba Sarki masoya!
A game da wannan shiri nasu na sharri, da muke da cikakken labari a kan sa, shekaran jiyan nan har Malam Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda kowa yasan alakar sa da kusancin sa da ‘yan shi’a, ya fitar da wasu rubuce-rubuce, da jawabai na sauraro, na batanci da karya ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
To ka sani, Malam Abduljabbar, na bibiyi maganar ka, amma hakikanin gaskiya na ga babu Komai a cikin ta sai tsantsar hassada da kin gaskiya da nunkufurci, da kuma kaucewa hakikanin abun da ya kamata kayi na fahimtar da al’ummah gaskiya. Sannan a cikin jawaban ka kowa zai fahimci cewa kai mutum ne mai alfahari da jiji-da-kai da sunan ilimi, wanda wannan ba dabi’a ce ta malaman Allah ba.
Domin kana ikirarin cewa wai duk fadin Jihar Kano, an kasa samun malamin da zai fito ya tare ka akan maganganun ka, saboda wai malaman sun san da cewa kafi karfin su, shi yasa ba za su iya tunkarar ka ba. Sannan kace wai duniyar Musulunci irin ka a yau ta ke bukata. Wai kuma kana gayyatar Mai Martaba Sarki domin kuyi mukabala, kuyi tattaunawa ta ilimi. Abduljabbar, ka manta wahalar da ka sha, a hannun dan uwa Sheikh Alkasim Hotoro, a lokacin da kuka yi mukabala, lokacin da ka kwashi kashin ka a hannu, shine yanzu kake kokarin nuna rashin kunya ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II?
To amma ni dai duk a cikin wannan soki-burutsu naka da shirmen ka, babban abun jin dadi na shine, ire-iren ku, marasa tawadu’u ga Allah, duniya ta san da ku. Domin kawai kuna neman suna ne, ta hanyar fitowa ku kalubalanci manyan mutane masu mutunci da daraja, manyan bayin Allah, irin Mai Martaba Sarki. Sannan duniya ta san cewa kun mayar da addinin Allah hanyar kasuwanci da samun abun duniya, ina rokon Allah ya shirye ka da mu baki daya, amin.
Malam Abduljabbar, ka sani Mai Martaba Sarki ba yayi karatu ne domin riya, da alfahari da raina jama’ah ba; karatun sa na ikhlasi ne da tsoron Allah, da kuma ciyar da al’ummah gaba. Don haka, Mai Martaba ba ya da lokacin biye wa ire-iren ka, domin wallahi, ni na san da cewa, Mai Martaba Sarki, ko kallon ka ba zai yi ba, balle har ya saurare ka, ko ya amsa maka akan wannan soki-burutsu da shirme naka.
Ya ku ‘yan uwa, abun da kowa ya sani ne, Mai Martaba Sarki yana da makiya da magabta kala-kala, iri-iri, daban-daban: a cikin masu sarauta akwai su, akwai su a cikin ‘yan siyasa da masu mulki, akwai su a cikin malamai, akwai su a cikin bokaye, ‘yan bori, da ‘yan tsibbu, sannan ga ‘yan shi’a da sauran su. Amma dukkanin su, abun da Mai Martaba Sarki yake rokon Allah game da su, shine Allah ya shirye su, ya ganar da su gaskiya, kuma ya ba su ikon bin ta. Ku sani, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II baya nufin kowa da sharri. Kuma shi bai riki komai ba in ban da Allah Subhanahu wa ta’ala. Don haka duk wanda ya riki Allah har kullun, shine MAI NASARA a cikin dukkanin al’amurrah!
Daga karshe, ina kira gare mu baki daya, da mu sa ikhlasi, gaskiya da tsoron Allah a cikin dukkanin lamurran mu. Idan mun yi haka, ina mai tabbatar muna da cewa za mu gagari duk wani shedani da makiri, mutum ne shi ko aljan. Amma idan babu gaskiya, ikhlasi da tsoron Allah a cikin lamurran mu, sai ka ga an ci nasara a kan mu, sannan abu kadan sai ya firgita mu. Idan Allah ne kadai abun tsoron mu, to mun fi karfin mu ji tsoron wata halittar Allah!
Allah yasa mu dace, ya kare muna shugabannin mu, ya tsare muna su daga dukkanin sharrin masu sharri, amin.
Nagode,
Dan uwan ku,
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto wannan sako daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za ku iya samun liman ta wannan adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma wannan lambar: 08038289761.