Sarki Sanusi II: Damo Sarkin Hakuri, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwa! Bayan karkasuwar hakuri, Malamai sun fassara shi da cewa, shine mallakar rai daga rashin yin juriya da yawan kuka, da kame harshe daga kai kara, da kaucewa daga cutar da kai ko cutar da wasu a lokacin jarabawa da masifa; da hana rai tayi wani mummunan tunani, sai abinda Allah ya yarda da shi, da hana harshe kada ya fadi komai mummuna a lokacin jarabawa ko wata masifa, sai abinda Allah ya yarda da shi, da hana gabban sa su aikata komai sai abinda Allah ya yarda da shi.

Wasu Malamai suka ce hakuri shine mallakar zuciya da harshe da gabbai akan bin umurnin Allah da hanuwa daga hanin sa, da kuma mallakar su a lokacin jarabawa ko masifa, kada su aikata komai sai abinda Allah ya yarda da shi.

Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Ya bayin Allah! Hakuri shine babban sinadari da Allah ya tarbiyantar da dukkan Annabawa da Manzannin sa akai, har suka ci nasara akan magautan su, suka isar da sakon Allah. Shi yasa Manzon Allah (SAW) ya zama shine shugaban dukkan masu hakuri a cikin halittun Allah baki daya.

A lokacin tsananin jarabawa, damuwa da yanke kauna, Musulmi su kan nemi kwanciyar hankali da natsuwa da shiriya ta hanyar yin hakuri da karanta zancen Allah, wato Alkur’ani. Allah Mai girma da daukaka ya sanar da mu cewa lallai za’a jarabi mutane a rayuwa, sannan ya umurce su da su jajircewa wannan jarabawa da yin hakuri, da rokon Allah. Hakika Allah ya tunatar da mu cewa ya jaraba imanin wadanda suka gabace mu, da jarabawa iri-iri, domin ya jarabi imanin su. Sannan ayoyin Alkur’ani da dama, masu tarin yawa sun tunatar da mu akan mu zamanto masu hakuri a lokacin wannan jarabawa. Misali, Allah Madaukaki yace:

“Ku nemi taimako da yin hakuri, da Sallah: kuma lallai ne ita, hakika mai girma ce face fa akan masu tsoron Allah.” [Bakara: 45]

Kuma Allah yace:

“Ya ku wadanda suka yi imani da Allah! Ku nemi taimako da hakuri da Sallah. Lallai ne, Allah na tare da masu hakuri.” [Bakara: 153]

Kuma Allah yace:

“Kuma lallai muna jaraba ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da nakasar dukiya da asarar rayuka da ‘ya ‘yan itatuwa. Kuma kayi bushara ga masu hakuri. Sune wadanda idan wata masifa ta same su, sai su ce: lallai mu daga Allah mu ke, kuma lallai gare shi za mu koma. Wadannan akwai albarka a kan su daga ubangijin su da wata rahama. Kuma wadannan su ne shiryayyu.” [Bakara: 155-157]

Sannan Allah yace:

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri kuma ku yi juriya, kuma ku yi zaman dako, kuma ku yi takawa, tsammanin ku za ku ci nasara.” [Ali Imran: 200]

Kuma ya sake cewa:

“Kuma ka yi hakuri, lallai Allah ba ya tozartar da ladar masu kyautatawa.” [Hudu: 115]

Kuma ya sake cewa:

“Kayi hakuri, kuma hakurin ka bai zamo ba face domin Allah, kuma kar ka yi bakin ciki saboda su, kuma kar ka kasance a cikin kuncin rai daga abin da suke yi na makirci.” [Isra’: 127]

Kuma dai ya sake cewa:

“Ka yi hakuri, lallai alkawarin Allah gaskiya ne. Kuma ka nemi gafarar zunuban ka, kuma ka yi tasbihi game da gode wa ubangijin ka, safe da yamma.” [Ghafir: 55]

Sannan Allah yace:

“Kuma ba za’a cusa wa kowa wannan hali ba face wadanda suka yi hakuri, kuma ba za’a cusa shi ba face ga mai rabo mai girma.” [Fussilat: 35]

Sannan kuma Allah yace:

“Lallai mutum yana cikin hasara, face wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayukkan kwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin hakuri (su kam ba su cikin hasara).” [Asr: 2-3]

Kuma Allah Madaukaki yace:

“Mun sanya shugabanni daga cikin su, suna shiryarwa da umurnin mu, a lokacin da suka yi hakuri, kuma sun kasance suna yin yakini da ayoyin mu.” [Sajdah: 24]

Sannan kuma yace:

“… Masu hakuri kawai ake cika wa ladar su ba tare da wani lissafi ba.” [Zumar: 10]

Sannan yace:

“… Kuma idan kun yi hakuri kuma kuka yi takawa, to sharrin su da makircin su ba zai cutar da ku da komai ba. Lallai Allah ga abun da suke aikatawa mai kewayewa ne.” [Ali Imran: 120]

Sannan bayan wannan, Manzon Allah (SAW) ya bayyana muna alkhairi da ake samu a cikin yin hakuri, a cikin ingantattun Hadisan sa, ga kadan daga cikin su:

1. Hakuri a lokacin jarabawa, bala’i da Masifa yana daukaka darajar bawa da matsayin sa a wurin Allah. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Lallai bawa zai samu wani matsayi da daukaka a wurin Allah, wanda bai same shi don yawan ibada ba sai dai don jarabawa da Allah yayi masa a cikin jikin sa da dukiyar sa da iyalin sa, sai yayi hakuri sai Allah ya daukaka matsayin sa a wurin sa saboda hakurin da yayi.” [Sheikh Albani ya fitar da shi a Sahih Abi Dawud]

2. Hakuri shine babbar kyauta mafi alkhairi. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Dukkan wanda yayi hakuri shima Allah zai hakurtar dashi; ba’a taba bai wa bawa wani abun kyauta mafi yalwa da alkhairi kamar hakuri ba.” [Bukhari]

3. Yin hakuri akan jarabawar da Allah ya dora maka zai kai mutum zuwa Aljannah. Ibn Abbas (RA) yace wa Adda’:

“Shin ba zan nuna maka wata mata daga cikin ‘yan Aljannah ba? Sai nace Eh, sai yace: “Waccan bakar matar da ta zo wurin Manzon Allah (SAW) ta ce: “Ina yin farfadiya kuma ina yin tsiraici ka roka man Allah”, sai Manzon Allah (SAW) yace: “Idan kin so za ki iya yin hakuri kina da Aljannah, idan kuma kin so in roka maki Allah ya baki lafiya? Sai ta ce: “Nayi hakuri, amma ka roka man Allah domin in daina yin tsiraici.” Sai yayi mata Addu’a.” [Bukhari da Muslim]

4. Hakuri akan wata masifa ko jarabawa da Allah ya dora maka sakamakon sa shine Aljannah. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Allah madaukakin Sarki yana cewa: Idan na jarabci bawa na da rasa masoyan sa guda biyu sai in musanya masa da Aljannah (yana nufin idan ya rasa idanun sa guda biyu, kuma yayi hakuri).” [Bukhari]

5. Hakuri shine mafi alkhairi a rayuwar masu imani. Manzon Allah (SAW) yana cewa:

“Kayi mamakin al’amarin mumini, lallai al’amarin sa dukkan sa alkhairi ne, babu wanda zai sami wannan halin da matsayin sai mumini. Idan masifa ta same shi sai yayi hakuri sai hakurin ya zama mafi alkhairi a gare shi, idan kuma ya samu jin dadi sai ya godewa Allah sai hakan ya zama mafi alkhairi a gare shi.” [Muslim]

Sannan duk bayan wannan, Allah Madaukaki ya sanya muna hakuri a matsayin wata kyauta marar iyaka da kuma hanya ta cin nasara a duniya da lahira. Domin lallai cin nasara yana tare da hakuri. Kuma lallai dukkan farin ciki yana biyowa bayan bakin ciki. Kuma dukkan tsanani yana tare da sauki. Kuma lallai Allah yana son masu hakuri.

Yaku jama’a! Lallai na san da cewa yana da matukar wahala, kuma ba zai yiwu ba ace, irin yadda Dan Adam yake kallon aikin jahilci da wawanci da tabargaza, da jahilai da wawaye suke yi a cikin al’ummar sa, amma ace abun bai dame shi ba, ko ace baya bakin ciki da abubuwan da suke faruwa. Lallai dole ne mumini ya shiga damuwa game da wadannan al’amura. Amma sai Allah ya umurci muminai da yin hakuri, da yin tawakkali ga Allah; sannan ya umurce su da kar su zamo masu yanke kauna daga rahama, agaji da kuma taimakon Allah. Daga cikin abun da zai taimakawa mumini a wannan lokaci na jarabawa, shine, ya kara yarda da Allah, kuma ya yawaita ayukkan alkhairi, sannan ya tsaya, ya jajirce akan gaskiya ba tare da tsoron kowa ba sai Allah, musamman wurin kokarin kwatar hakkin sa da ‘yancin sa wurin masu kokarin zaluntar sa.

Ya ku ‘yan uwa! Wadannan ayoyin Alkur’ani Mai girma da Hadisan Annabi (SAW) da maganganun Malamai da suka gabata, suna tabbatar muna da matsayin hakuri da kuma muhimmancin sa a cikin addinin Musulunci.

Alhamdulillah, muna godiya ga Allah Madaukaki, domin wannan umurni da yayi shi da Manzon sa (SAW) game da yin hakuri akan jarabawa, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II yana akan sa dodar.

Domin al’ummar jihar Kano sun shaida, ‘yan Najeriya sun shaida, haka duniya ma ta shaida, cewa, Mai Martaba Sarki mutum ne mai juriya da hakuri. Domin duk wani nau’i na cin amana, cin mutunci da wulakanci, wallahi babu wanda Gwamnatin Jihar Kano da ‘yan kanzagin ta ba su yi masa ba. Sun muzguna masa, sun ci amanar sa, sun toshe masa duk wasu hanyoyin samun kudaden tafiyar da harkokin mulkin masarautar Kano, sun dauki hayar zauna gari banza, ‘yan tamore, marasa aikin yi, suna biyan su makudan kudade, don suyi ta yin rubuce-rubuce a soshiyal midiya da nufin bata sunan Mai Martaba Sarki, da yi masa karya, sharri, kage da kazafi, amma duk bawan Allah nan yayi hakuri, ya jure, ya dake, ya dogara ga Allah, bai kula su ba. Kai har idan ma mutanen sa da jama’ar sa suka yi magana, ba abun da zai ce da su illa kuyi hakuri, komai yana da iyaka. Sarki bai taba umurtar wani mutum ya dauki wani mataki na kare shi ba.

Sun yi kokarin yi wa Mai Martaba Sarki sharri da kazafin wai yayi almubazzaranci da kudaden masarauta, amma sun manta da cewa duniya tana kallon su ne tana yi masu dariya, domin ta dauke su shashashu. Idan ba haka ba, mutumin da shi a rayuwar sa baki daya a cikin wuraren hada-hadar kudade ne yayi aiki, wato bankuna, amma ya gama lafiya, ba’a taba zargin sa da sata ko almundahana ba; yayi aiki a banki daban-daban har zuwa lokacin da Allah yasa ya rike Gwamnan babban bankin Najeriya, wanda nan ne taskar ma’ajiyar kudin kasar nan, amma duk ya gama lafiya, babu maganar zargin yayi sata, sai yanzu da ya zama Sarki, anan ne wai zai taba dan canjin gudanar da masarautar Kano? Haba jama’ah! Wallahi ai ko mahaukaci, wawa ko jahili ba za su taba yarda da wannan karyar ba!

Duk mai bibiyar soshiyal midiya, wallahi yana ganin yadda Gwamnatin Jihar Kano da magoya bayan ta suke zagi da cin mutuncin Mai Martaba Sarki, amma dai duk wannan Dan taliki ya daure, ya hakura, ya jure wa wannan wawanci da rashin mutunci na su.

Saboda haka, da yardar Allah, mun yi imani, Mai Martaba Sarki zai samu cikakkiyar lada da kyakkyawan sakamako da Allah yayi alkawarin zai ba wa masu hakuri. Sannan nasarar da Allah yayi alkawarin zai bai wa masu hakuri, mun yi imani Mai Martaba Sarki zai ci nasara akan dukkanin masu bin sa da sharri.

Alhamdulillah, ai ko yanzu ma Mai Martaba Sarki yaci nasara, tun da duniya ta fahimci, kuma ta yarda cewa lallai shi mutum ne mai hakuri. Sannan kuma bayan an fahimci shi mai hakuri ne, abu na biyu shine, duniya ta fahimci cewa, lallai shi ake zalunta a cikin wannan badakala! Sanadiyyar haka, sai Allah Madaukaki ya mayar da Mai Martaba Sarki kamar gwal, wato zinari; kullum ana kokarin hada masa zafi, amma yana kara yin fice a duniya, Allah yana kara daukaka darajar sa, kuma Allah yana kara masa masoya. Kun san shi zinari, a lokacin da ake hada masa wuta, to lokacin ne yake kara yin haske.

Sannan kuma ku sani fa, yanzu ta bayyana a fili cewa, wannan daraja da daukaka da ci gaba da Mai Martaba Sarki yake samu anan gida Najeriya da kuma duniya baki daya, abu ne da tabbas yana yi masu ciwo, shi yasa saboda hasada da ganin kyashi, wai suka sha alwashin dakatar da wannan daukakar. Amma sun manta da cewa al’amarin daga Allah ne, sun manta yin Allah ne ba yin mutum ba!

Daga karshe, mu dai kiran mu zuwa ga al’ummah shine, kuci gaba da tsayuwa akan gaskiya komai wahala, kuma komai rintsi. Sannan ku ci gaba da yiwa Mai Martaba Sarki Addu’a, domin ita ce makamin mumini.

Sannan kuma wallahi, kar ku taba yarda da keta rigar mutuncin masarautar Kano. Domin wannan masarautar da duk sauran masarautun mu masu daraja, kokari ne na jihadi da gwagwarmayar Shehu Usman Dan Fodio. Idan har kuka yarda da son zuciyar wasu ‘yan siyasa, marasa kishi, suka rusa wannan masarauta, to ku aka rusa da kuma ainihin tarihin ku. Kar ku taba yarda da su, domin masarauta daya ce aka sani a Kano. Duk wata masarauta da ba ta Kano ba ku dauke ta shirme. Kar kuji tsoro ko shakkar wani ko wasu mutane. Kuma kar ku yarda wani ya bude maku ido, ko ya zare maku ido, domin shi ba Allah ba ne. Allah ne ya halicce ku ku da shi. Kuma ku sani, rayuwar ku da abincin ku duk yana hannun Allah ne, ba hannun wani mutum ba.

Sannan duk wani tsari na kokarin jefa Jihar Kano cikin rikici da rudani, sam kar ku yarda da shi. Ku nuna wa duniya cewa ku Kanawa mutane ne masu kaunar zaman lafiya da ci gaba, don haka ku nuna masu kuna kaunar Sarkin ku, abar ku da Sarkin ku kawai!

Sannan ina kara kira da tunatar da mu cewa, muci gaba da Addu’a, kada mu saurara, muyi ta yi a gidajen mu da Masallatan mu da Makarantun mu da wuraren tarurrukan mu, domin cin nasarar Mai Martaba Sarki daga sharri da makircin wadannan mutane.

Kar mu yi nufin kowa da sharri, amma mu roki Allah, dukkan masu nufin Mai Martaba Sarki da sharri, ko su waye, Allah ya mayar masu da sharrin su a kan su. Wannan shine!

Ya Allah ka azurta mu da yin hakuri, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau. Ya rubuto wannan sako daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.

Share.

game da Author