Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da UN-Water sun yi kira ga kasashe masu tasowa da su ware kudade masu tsoka domin kula da harkar taftace muhalli da samar da ruwan sha mai tsafta.
Yin haka zai taimaka wajen inganta kiwon lafiya na mutane da al’umma baki daya.
Hukumar WHO da hukumar samar da tsaftataccen ruwa na majalisar dinkin duniya (UN-Water) sun yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da UN-Water ta yi game da illar rashin samar da tsaftataccen ruwan sha da muhalli a kasashe masu tasowa.
Binciken ya nuna cewa rashin samar da tsaftaccen muhalli da ruwan sha na da nasaba da karancin kudade da ake ware wa wadannan fannoni ne da kuma rashin ma’aikatan da suka kware wajen samar da irin wadannan kula ga mutane.
Idan ba a manta ba a watan Yuli ne jami’in asusun kula da al’amuran kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Bioye Ogunjobi ya bayyana cewa wanke hannu da ruwa ba tare da Sabulu ba baya kau da dattin a hannu.
Ya ce rashin amfani da sabulu da ruwa wajen wanke hannun musamman bayan an fito daga bayan gida shine ya fi dacewa ba da ruwa ba kawai.
Ya kuma yace kafin a ci abinci da bayan anci a wanke hannu da ruwa mai tsafta da sabulu domin samun kariya daga kamuwa da cututtuka.
Sannan ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa wanke hannu da ruwa da sabulu na kare mutum daga kamuwa daga mugan cututtuka.