Salsalar yadda aka janyo wa Najeriya asarar Naira tiriliyan 3.2

0

Shugaban Kamfanin P&ID wanda aka kulla yarjejeniyar kwangilar aikin gas (GSPA) din da ke neman janyo wa Najeriya asarar naira tiriliyan 3.2, ya yi bayani a karon farko dangane da yadda ya samu aikin kwangilar.

Ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da Ministan Shari’a Abubakar Malami ke ta kokarin tsame Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari daga laifin sakacin da ake cewa tayi na kin yarda a sasanta da kamfanin P&ID.

Malami ya ce diyyar da aka yanka wa Najeriya ta naira tiriliyan 3.2 rashin adalci ne, kuma za su kalubalance ta a kotun.

Ya ce tun farko dama an kulla yarjejeniyar kwangilar ba da nufin ta yi nasara na.

Da ya ke bayani, Shugaban Kamfanin P&ID, Micheal Quinn ya ce ba da rana tsaka kawai ya yanki takardar gwangila ba. Sai da ya bi hanyoyin da suka dace tukunna.

“Sai da mu ka yi zama da Shugaban Kasa na wancan lokacin tukunna, marigayi Umaru ‘Yar’adua. Tare da Ministan Mai na Lokacin, Rilwan Lukman da kuma Shugaban NNPC na lokacin, Shehu Ladan tare da wasu mutane 15.

Quinn ya ce bayan an shirya kwangilar a lokacin Yar’adua na ya na kwance asibiti ya na jiyya, bai dade ba sai ya rasu.

” Rasuwar Umaru ke da wuya sai muka sanar da Jonathan, Diezani da Mashawarcin Jonathan kan harkokin fetur, Mista Egboghah batun kwangilar da aka kulla da P&ID.

Daga nan Jonathan ya amince a sasanta. To a ranar 19 Ga Satumba, 2012, muka sanar da Gwamnati cewa mun nada lauya Anthony Evans a matsayin wakilin mu da za a yi zaman sasantawar da shi a kotun Amurka.

A ranar 30 Ga Nuwamba, 2012 Gwamnatin Najeriya ta aiko mana da cewa ta nada Bayo Ojo, ministan shari’a na lokacin ya wakilce ta.

“Wadannan bangarori uku ne suka zauna suka gamsu da cewa Najeriya ta karya ka’idar kwangilar da aka kulla yarjejeniya tsakanin ta da P&ID.

Michael Quinn ya bayyana sunayen wasu mutane da ya ce na da masaniya dangane da kwangilar. Sai dai kuma ya ce ba lallai ba ne a ce duk su na laifi:

” Marigayi Yar’adua, Rilwanu Lukman, Diezani Maduekwe, Olatunde Odusina, Emmanuel Egbogha, Shehu da Ladan, Labi Ajibade.

Akwai kuma irin su Goni Sheikh, Grace Taigo, David Ige, Mista Jones da wasu da dama.”

Tuni dai har an fara lissafa irin kudade da dukiyar Najeriya da za a kwace a Amurka da Birtaniya idan har tura ta kai bango.

Share.

game da Author