‘Sakin Layin’ da Buhari ya yi a UN ya jawo ce-ce-ku-ce a Shafunan Yanar-Gizo

0

Wani bidiyo da aka nuno Shugaba Muhammadu Buhari na bayar da karkatacciyar amsa bambarakwai a Majalisar Dinkin Duniya (UN), ta haifar da ce-ce-ku-ce tare da caccaka da gwasale shugaban kasar a soshiyal midiya.

An yi wa Buhari caa, jin yadda aka yi masa wata tambaya, amma kuma ya bayar da wata amsa daban, wadda ba a kan tambayar da aka yi masa ba, kuma ba su ma yi kamanceceniya da juna ba.

Al’amarin ya faru ne a jiya Laraba, a birnin New York wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, na 74.

A wurin taron tattaunawar dai akwai mashahuran mutane, ciki har da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres.

Yayin da ana natsa ana tambaya da amsa, sai aka tambayi Buhari kamar haka: “Shugaba Buhari, daga adadin yawan al’ummar Najeriya akwai yara masu tarin yawa. Shin ya ka ke makomar su za ta kasance nan gaba? Amma fa da Turanci aka yi masa wannan tambaya.

Nan da nan shi kuma Shugaba Buhari sai ya kama karanta amsar, wadda tuni an rigaya an tubuta ta.

Sai dai kuma amsar da ya bayar a kan batun canji yanayi ko dumamar yanayi ya yi magana, ba a kan abin da aka tambaye shi ba.

“Ya ku masu girma, maza da mata, ra’ayi na ya yi daidai da na Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya cewa duniya gaba daya ta na fuskantar mummunar barazanar canjin yanayi. Ba sai an yi wata tantama ba, wannan canjin yanayi kuwa duk dan adam ne da kan sa ya haddasa shi.

A haka Buhari ya ci gaba da karanto batun dumamar yanayi daga cikin takardar jawabin da ya karanta a Zauren Majalisar Dinkin Duniya. Har ya zarce inda ya ke cewa:

“Za mu dauke kwakkwaran matakin kirkiro hanyoyin shawo kan canjin yanayi, ta hanyar yin amfani da matasa wajen dasa itatuwa milyan 25….”

Ya kuma gangara harkan batun samar da hasken lantarki daga manyan madatsun ruwa, hasken ‘solar’ da matun makamashin nukiliya da ma harkokin makamashi bai daya.

Kai sai da ta kai Buhari har ya shiga karanto batun halin da Tabkin Chadi ke ciki da kuma kokarin da ake yi wajen farfafo da yankin.

Sakin Layi

Dukkan wannan amsa da Buhari ya bayar ta na cikin jawabin sa da ya karanta a Majalisar Dinkin Duniya, kuma kafafen yada labarai duk suka buga, ciki har da PREMIUM TIMES.

Tolu Ogunlesi, daya daga cikin hadiman Buhari a kan kafafen yada labarai na ‘online’ ne ya fi shan caccaka, domin shi ne ya fara tura bidiyon tambayar da amsa a shafin sa na Twitter, wanda nan da nan aka yi masa caa, ana caccakar sa da kuma Shugaba Buhari.

Cikin wadanda suka fara suka a sahun farko, har da Gimba Kakanda da kuma Obey Ezekwesile.

Waiwaye

Ba wannan ne karo na farko da Buhari ya fara kwafsawa a cikin taro ba. Yayin da wasu ke ganin abin na da nasaba da tsufa, wasu kuma na danganta abin da mantuwa.

Cikin watan Yuni, 2015, a taron G7 a kasar Jamus, Buhari ya kira Shugabar Jamus da suna ‘Shugabar Jamus ta Yamma. Alhali kuma tun cikin 1990 babu wata Jamus ta Yamma balle ta Gabas, an hade su.

Hatta sunan ta ma bai ambata daidai ba. Sannan kuma kuma ita mukamin ta ‘Chancellor’ ce, ba ‘President’ ba kamar yadda Buhari ya kira ta.

 A lokacin yakin neman zaben Shugaban Kasa, Buhari ya yi subul-da-baka a Zamfara, inda bayan ya kammala jawabi, ya ce: “Allah ya ba mu damina mai albarka, a samu abinci. … idan an ci an koshi, duk fitinar da a a yi, a je a yi ta yi.”

Share.

game da Author