Sai da shaidar yin rajistar katin zama dan kasa zaka rubuta jarabawar JAMB – Hukuma

0

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta bayyana cewa daga yanzu rubuta jarabawar JAMB sai dalibi na da mallakin katin zama dan kasa ko kuma lambar yin rajistar mallakar katin wato ‘NIN’ da hukumar NIMC ke badawa.

Kakakin hukumar Fabian Benjamin ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jihar Legas ranar Talata yana mai tunatar da mutane cewa tuni har hukumar gta fara saida fom din jarabawar na shekarar 2020.

Benjamin ya ce JAMB ta shirya wannan tsari ne domin toshe kafafen da dalibai kan bi don yin satar jarabawa.

“A dalilin haka muke kira ga dalibai da su tabbata sun yi rajista da hukumar NIMC domin samun labar NIN saboda rashin shi zai sa a hana mutum rubuta jarabawar. Sannan duk sunnan da dalibi ya yi amfani da shi a wajen yin rajistan katin zama dan kasa da shi ne JAMB za ta yi amfani da.

“ Da yanzu za a rika yin rajistan jarabawar JAMB ne wuraren yin rajistar da hukumar NIMC ta bude ko kuma ta amince da su a fadin kasarnan.

Benjamin yace ga daliban da suka yi rajistan JAMB kuma suka karbi lambar NIN kafin shekarun su ya kai 16 za su iya komawa hukumar domin karban wani lambar yanzu da shekarun su ya kai.

Ya ce dalibai za su iya komawa wajen yin rajistan katin dan kasa domin karban lambar NIN a duk lokacin da suka batar da lambar ko kuma su latsa *346# a wayar domin samun lambar NIN din nasu.

“Za a ga lambar *346# ne a bayan katin yin rajistar jarabawar JAMB din da aka siya’’.

Share.

game da Author