Ronaldo ya sake kafa tarihi

0

Dan wasan kwallon kafar kasar Portugal, wanda ke buga wa kungiyar Juventus na Italiya, Cristiano Ronaldo, ya sake kafa tarihi a wasan kwallon kwafa.

A wasan da Portugal ta buga na neman tsallakewa shiga gasar Cin Kofin Turai na 2020, Ronaldo ya zazzaga kwallaye hudu a ragar kasar Lithuania.

An dai tashi wasan Portugal na da 5, ita kuma Lithuania na da 1 tal.

Wadannan kwallaye da Ronaldo ya jefa, sun kai shi ga cin kwallaye 93 kenan a yawan wasannin da ya buga wa kasar sa, Portugal.

Sannan kuma a yanzu kenan Ronaldo ya jefa kwallaye a ragar kasashe dai-dai har 40 na duniya.

Har ila yau, Ronaldo ya jefa kwallaye 25 kenan a wasannin share fagen Gasar Kofin Turai.

Wadannan kwallaye 4 da ya ci a wasa daya, sun kai shi ga cin kwallaye uku ko sama da haka sau takwas kenan a wasannin da ya buga wa kasar sa Portugal.

A tarihi dai Ali Daei ne kadai, dan kasar Iran ya fi Ronaldo cin kwallaye a wasannin kasa da kasa.

Daei ya ci wa Iran kwallaye 109 a wasannin da ya buga tsakanin Iran da kasashen Gabas Ta Tsakiya.

SAURAN WASANNI:

A ci gaba da wasan share fagen neman zuwa Gasar Kofin Turai na EURO 2020, Ingila ta caskara Kosovo da ci 5:1, ita kuma Faransa ta lallasa Andora da ci 3:0.

Wasannin sada zumunta a aka buga a tsakanin wasu kasashen Latin Amurka, Ajentina ta ragargaza wa Mexico ci 4:0. Sai Brazil da ta sha kashi a hannun Peru da ci 0:1. Yayin da Amurka a gida ta yi kunnen doki 1:1 ita da Uraguary.

Share.

game da Author