Ranar da nafi zama cikin bacin rai da tashin hankali – Sarki Sanusi

0

” Ina zaune a fada wata rana sai naji wata mata na kuka a wajen fada. Hankali na sai ya karkata ga wannan wannan mata na sa a shigo da ita inji ko me take tafe da shi. Bayan an shigo da Ita sai naga ta na kuka ashe wai dan ta ne ya rasu a hannun ta a wannan lokaci. Da na tambaye ta yaya aka yi haka sai tace ta yi ta kokarin ta ganni in taimaka mata da naira 3000 ta kaishi asibiti domin bashi da lafiya. A kokarin ta samu daman haka ne Allah bai sa zan ganta ba har dan ya cika.

” Wannan abu ya tada mini da hankali matuka domin zan iya cewa a tsawon zama tun darewa kujerar mulkin Kano babu wani abu da ya taba tada min da hankali sannan na kasa mantawa dashi har yanzu irin wannan abu.

Sarki Sanusi ya ce talauci da tsananin yunwa shine mutane ke fama dasu a kasar nan da dole sai gwamnati ta maida hankali matuka domin sama wa mutane sauki da kuma kafa ma’aikata na musamman domin kula da kauda matsalolin tsananin yunwa ga musamman yara kanana.

Sarki Sanusi ya fadi haka ne a jawabinsa da yayi babban taron kungiyar NSN wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na wannan kungiya.

Ya kara da cewa ” Dole sai gwamnati ta karkato da akalarta wajen inganta fannin kiwon lafiyar yara kanana da kafa hukumomi da zasu rika kula da shayar da yara abincin da zai rika gina musu jiki da kuma kau da matsanancin yunwa da talauci a tsakanin mutane.

Sannan kuma yace wani abu dake ci masa tuwo a kwarya shine yadda jiharsa, wato jihar Kano ke akan gaba wajen fama da matsalolin matsanancin yunwa ga yara kanana da tsananin talauci. “Hakan na sa ana yawan rasa yara kanana da mutuwar uwaye.”

Matakan da gwamnati ta dauka

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace gwamnati ta maida hankali matuka wajen ganin an kawo karshen wannan matsala da ake fama dashi.

Babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya Abdullahi Abdulaziz wanda shine wakilci mataimakin shugaban kasa a taron yace cikin shirye-shiryen da gwamnati tayi sun hada da ciyar da yara a makarantun boko sannan ta ware kudade domin siyo magungunan na maganin yunwa ga yara. Sannan kuma da shirin ciyar da mata masu ciki, masu shayarwa da masu ciki.

Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yunwa na daga cikin matsalolin dake hallaka yara kanana a kasar nan.

UNICEF ta kara da cewa akalla yara miliyan biyu a a Najeriya na fama da yunwa sannan biyu cikin yara 10 dake fama da yunwa ne kawai ke samun kulawa ko kuma tallafi.

Share.

game da Author