Tsohon gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, ya saida dukkan hannayen jarin sa da ke bankin First International Banking (FIB) Group Limited da ke Gambia. Haka PREMIUM TIMES tabbatar.
Wasu takardun sirri masu dauke da yarjejeniyar sanarwar sun tabbatar da cewan cikin 2015 zuwa 2016 aka cefanar da bankunan.
Takardun na sirri da wata jaridar Jamus ce mai suna Suddeutsche Zeitung da kuma International Consortium of International Journalists, ICIJ da kuma wasu kafofin fallasa sirruka na Appleby da Asiaciti Trust tare da hadin kan wasu kafofin fallasa sakonninin sirri su 19 fadin duniya.
Kada kuma a manta, PREMIUM TIMES na daga cikin kungiyar kafafen fallasa bayanan sirrin na duniya, da suka fallasa wasu boyayyun kadarori da kamfanoni da wasu attajirai ke boyewa a kasashen duniya, wato ‘Paradise Papers.’
Takardun bayanan cinikin sirrin sayar da bankuna da Kalu yay i, sin nuna cewa wata cibiyar hada-hada ce da ke Amurka, mai suna Lilium Capital ta sayi bankunan.
Wannan cibiyar hada-hadar zuba hannayen jari dai hedikwatar ta na birnin New York, Amurka.
FIB Group Limited da ke Gambiya ke da nauyin gudanar da hada-hadar kasuwancin hannayen jari da bankuna a kasashen Gambita, Saliyo, Liberiya, Sieera Leonne, DRC da Congo.
Kafin wannan cinikin kuwa, kamfanonin Slok Nigeria Limited da IICL ke da kashi 80 bisa 100 na hannayen jarin FIB.
Dalla-dallar takardun bayanan cinikin sun nuna cewa Lilium Capital ya saye FIB daga SLOK da IICL a kan kudi dala milyan 10.
Sannan kuma daga cikin jarjejeniyar, an amince Lilium Capital zai rika biyan SLOK da IICI Limited dala milyan daya a kowace shekara, har tsawon shekara biyar.
Wannan kamfani dai ya na da kamfanin Inshora a kasashen Liberiya, Sierra Leonne, Gambiya da Gini.
Kamfanin SLOK Nigeria dai mallakar Kalu ne, kuma ya na gudanar da harkokin kasuwanci a kasashen Afrika ta Yamma da dama.
Ya na harkokin fetur da gas, banki da hada-hadar kudade, kafafen yada labarai da wallafa takardu, cinikin manyan gidaje, da gina sabbin kantama-kantaman unguwanni da harkokin hada-hadar yawon bude ido.
Shi ke da jaridun The Sun da Daily Telegragh.
A nan Najeriya dai ana ci gaba da shar’ar zargin wawurar naira bilyan 7.2. Sai dai kuma cikin watan jiya ne Kalu ya kammala shigar da bayanan kare kan sa a kotu.
Wannan shari’a ta shafe shekaru 12 ana fafatawa. Kalu wanda a yanzu sanata ne a karkashin APC, ya musanta cewa ya handame kudaden jihar Abia.
Ya yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007.