Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya fi duka gwamnonin da aka taba yi a jihar Kaduna hangen nesa.
El-Rufai ya fadi haka ne da yake amsar tsohon mataimakin shugaban kasan a fadar gwamnati da ke Kaduna.
A jawabin sa gwamna El-Rufai ya jinjina wa Namadi bisa namijin kokarin da yayi da hangen nesan sa wajen kafa tubalin gini da samar da ruwan sha a Zariya.
” Baya ga ruwan Zariya daya fara aiki akai, ya fara gina babban asibiti mai cin gado har 300. Sannan maigirma Namadi Sambo ne ya shirya raya garin Kaduna da kewaye da bunkasa tsarin samar da nagartattun shirye-shirye domin mutanen jihar.
” Gwamnonin baya sune suka rikirkita jihar, suka saka ta cikin yanayin da ya sa gashi har yanzu muna ta fama da gyaran fasali da ayyukan jihar. Wasu daga cikin su sun maida jihar da asusun ta kamar kasuwanci sannan wasu kuma sune suka saka mu cikin wannan matsala da muke kokarin gyarawa.
” In banda kai Namadi, babu wani gwamna da ya yi wani abin a zo a gani. Domin kaine ka yi kololuwar hange inda ka rika tsara shirye-shirye da manufofin raya kasa da ci gaban jihar a lokacin da kake gwamna. Sai dai kuma kash, baka samu ka cimma burin ka ba kafin samun ci gaba da kayi na zama mataimakin shugaban kasa.
Namadi Sambo ya kai wa El-Rufai ziyarar godiya ne da jinjina bisa irin ayyukan da yake yi a jihar Kaduna tun bayan darewar sa kujerar gwamnan jihar Kaduna.