Bankin Duniya ya bayyana cewa ya na nan ya na tattaunawa da gwamnatin Najeriya dangene da bukatar kasar ta neman bashin zunzurutun kudi har dala bilyan 2.5.
Kudin dai an ce idan aka ciwo bashin, za a yi aikin inganta wutar lantarki ne da su.
Mataimakin Shugaban Bankin Duniya mai kula da kasashen Afrika, Hafez Ghanem ya bayyana haka a lokacin da ya ke wa manema labarai bayani a Abuja, ranar Laraba.
“Mu na magana a kan wani sabon bashin da Najeriya ke kokarin karba ne na dala bilyan 2.5.” Inji Ghanem.
Ya kara da cewa bashin zai sa tattalin arzikin Najeriya ya rika gogayya da na manyan kasashen duniya tare da habbaka masana’antu da kuma samar wa matasa ayyukan yi.
Sannan kuma ya ce bashin zai kara taimaka wa Najeriya ta fatattaki fatara da talauci da kara inganta rayuwar jama’a dama.
Kamar yadda ya kara furtawa, idan aka ciwo bashin za a kara maida hankali wajen samar wa mata ingantattun hanyoyin dogaro na sana’a da kuma ilmantar da kananan yara, ciki har da yara nakasassu.
Idan ba a manta ba, cikin 2018 sai da Najeriya ta ciwo bashin Dala bilyan 2.4 a Bankin Duniya.
Sannan kuma cikin 2018 sai da bankin ya bayar da dala milyan 486 domin inganta tashoshin wutar lantarki da gyaran wasu kananan tashoshin samar da wuta.
Sannan kuma gwamnatin tarayya ta sa hannun yarjejeniyar inganta wutar lantarki tsakanin ta da kamfanin Siemens yadda za a iya samun migawatts 25,000 nan da shekara ta 2025.
An sai tsara wannan kwangilar aiki ne tun cikin watan Agusta, 2018, lokacin da Shugabar Kasar Jamus, Angela Mikel ta kawo ziyara Najeriya.
Discussion about this post