Najeriya, Chadi da Nijar za su farfado da Tafkin Chadi

0

Kasashen Najeriya, Chadi da Nijar na wani kokarin aikin hadin-guiwar sake farfado da rayuwar al’ummar yankin Tafkin Chadi da kuma sake farfado da tafkin.

Babban Daraktan Hukumar Great Greean Wall, Bukar Hassan ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala wani taro na kasa-da-kasa a kan kwararowar Hamada, a jiya Lahadi a New Delhi, babban birnin kasar Indiya.

An ruwaito cewa a wurin taron wanda shi ne na 14 da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya domin lalubo yadda za a magance kwararar Hamada aduniya, an shafe makonni biyu ana gudanar da shi, tun daga 2 zuwa 13 Ga Satumba.

Ya ce tunda batun matsalar muhalli babu ruwan ta da tsayawa kan iyakar wannan kasar ta ki shiga waccan, haka kai tsakanin kasahen uku zai taimaka wajen farfado da harkokin noma, sake gina filaye ko gonakin da suka zaizaye da kuma gina al’ummar yankin Tafkin Chadi.

Ya ce tsare-tsaren za su hada da bijiro da dabarun noma na zamani, kiwon dabbobi a tsakanin kasashen uku wadanda suka yi kan iyaka da Tafkin na Chadi.

Babban Daraktan ya kara da cewa Tafkin Chadi wanda ya ke shimfide a kan kasa mai tsandauri, ya rasa kashi 90 bisa 100 na ruwan da aka san shi da su a cikin ‘yan shekarun nan. Dalili kenan noma a yankin ba shi da wata fa’ida a halin yanzu.

“A yau an daina noma gaba daya a Yankin Tafkin Chadi.

“Saboda haka nauyin wannan hukuma ce ta gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa mun sake samu ko dawo da yawan ruwan da muka rasa a Tafkin Chadi. Saboda kafewar rasa ruwan ya haifar da dimbin marasa aikin yi.

“Idan muka yi haka, masu gonakin da suka rasa wuraren noma saboda rashin ruwa a tafkin, za su sake samun gonakin su idan tafkin ya sake rayuwa.

“Sannan kuma za mu tabbatar da cewa an dasa itatuwa a dukkan tsawon kan iyakokin Tafkin Chadi. Tafkin Chadi na daya daga cikin yankunan da suka zaizaye a duniya, sannan kuma ga babbar matsalar dimbin al’ummar da suke cikin halin kuncin tashe-tashen hankulan da ya kara ragargaza yankin.

“Dalilin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ke so ya ga an sake farfado da Tafkin Chadi, saboda rikicin Boko Haram da ya addabi kasashe uku masu makwabtaka da Tafkin Chadi, duk su na fama da matsalar kafewar da tafkin ya yi.” Haka Hassan ya bayyana.

Daga nan a ce haka kuma Shugaba Buhari ya ba shi umarnin fara aikin dashen itatuwa samar da kandagarkin hamada gadan-gadan a jihohin Sokoto, Jigawa, Yobe, Barno da Katsina.

Ya ce matsalar lalacewar muhalli a yankunan ce ke sa matasa yin hijira daga Arewaci zuwa Kudancin kasar nan.

Share.

game da Author