Masana’antun Najeriya hudu za su fara sarrafa madara

0

A kokarin sun a koyi da tsarin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shigo da shi na kashe kasuwar shigo da madara daga kasashen waje, wasu masana’antu hudu na Najeriya sun fara sarrafa madara.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefile ne ya bayyana haka a jiya Alhamis yayin da ya ke bayyana sunayen masana’antun.

Masana’antun inji shi, sun hada da FrieslandCampina WAMCO, Neon Agro, Chi Limited da kuma Irish Dairy.

Ya ce dukkan su sun bayyana aniyar su ta bukatar zuba jarin samar da madara a Gandun Kiwon Dabbobi wato, Bobi Grazinga Reserve da ke Jihar Neja.

Wannan wuri ya na cikin Karamar Hukumar Mariga, inda aka kebe Gandun Kiwon Dabbobi har 26 a karkashin kudirin gwamnatin jihar Neja na inganta kiwon dabbobi, bisa hadin kai da Babban Bankin Najeriya, CBN.

Ya ce a gandun akwai akalla iyalan makiyaya masu kula da su har 700 a fili mai fadin eka 31,000.

Sannan kuma ya ce akwai shanu 300,000 da za a fara wannan shiri da su.

Sauran eka 3,000 kuma inji Emefile, gwamnatin jihar Neja ce za ta yi na ta aikin inganta kiwon shanun da samar da madarar a ciki.

Tun a ranar Talata Emefile ya ce daya daga cikin kamfanin, wato FrieslandCampina WAMCO ya gyara eka sama da 600 domin farawa.

Shi da Neon Agro za su yi amfani da eka 10,000 domin wannan gagarimin aikin samar da madara.

Kamfanin Chi Limited shi ne ya sa hannun yarjejeniya ta yin amfani da eka 4,000.

Akwai ofishin ‘yan sanda, asibitin dabbobi, makarantar firamare, sannan kuma akwai karamin asibiti da a yanzu ake kan aikin ginawa.

A jihar Kaduna kuma, Emefile ya ce tuni har an zuba jarin naira bilyan 12 domin irin wannan sana’a inda za a habbaka fili mai eka 6,000 a Gandun Kiwon Dabbobi na Damau Grazing Reserve.

Sannan kuma akwai kamfanin Arla a Kagarko da kuma kamfanin Prpmasidor Group da ya fara aikin gyaran eka 500 ta wurin samar da madara a Ikun Dairy Farm Project, a Jihar Ekiti.

Share.

game da Author