Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kwashi kashinta a hannu a karawa da tayi da kungiyar kwallon kafa ta Norwich a wasan Premier League ranar Asabar.
Norwich da doke Manchester city da ci 3-2.
Wannan nasara na Norwich tayi ya yi matukar ba masu kallon wasan Premier League mamaki ganin cewa Norwich tana kasa-kasa a tebur din ita kuma City ita ce ke rike da kofin Premier League din.
Haka kuma duk a wasan ranar Asabar kungiyar Chelsea ta lallasa Wolves da ci 5-2.
A kasar Spain kuma Real Madrid ta doke Levente da ci 3-2, Barcelona kuma ta doke Valencia da 5-2.