Mama Taraba ta koma PDP

0

Tsohowar ministan harkokin mata Aisha Alhassan, ‘Mama Taraba’ ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf domin koma wa jam’iyyar PDP daga UDP.

Idan ba a manta ba Aisha Alhassan ta rike kujerar ministan harkokin mata bayan nasarar da jam’iyyar APC ta yi a zaben 2015. Itace yar kararar gwamnan jihar Taraba a jam’iyyar sai dai kuma bata yi nasara ba a zaben a 2015.

Shugaba Buhari ya nada ta ministan harkokin mata a wancan lokaci.

Aisha ta sake neman tsayawa takarar gwamnan jihar Taraba a 2019 inda jam’iyyar ta ki amincewa ta takarar ta ki bata damar yin takarar a inuwar APC.

Daga nan sai ta fusata ta sauka daga kujerar ministan harkokin mata sannan ta fice daga jam’iyyar APC ta koma jam’iyyar UDP.

Jam’iyyar APC ta ce taki ba Aisha tikiti ne saboda ganinta da aka yi a wani Bidiyo tana kuranta tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sannan tana cewa shi take yi duk da a lokacin tana rike da kujerar minista a APC.

Tace magoya bayanta ne suka roke ta da ta canja sheka zuwa PDP a jihar Taraba.

” Ni mace ce mai sauraren kuka da kiran magoya baya na kuma duk wani abu da zan yi, ina yi don su ne saboda haka idan suka ce ga abinda suke so haka zan yi.

Yanzu dai an kafa kwamiti har guda biyu domin shirya bukin komawar Aisha PDP da kuma yin sallama da jam’iyyar UDP.

Share.

game da Author