Wasu Mahara dauke da manyan bindigogi sun kashe mutane biyu sannan wasu da dama sun jikkata a harin da suka kai kauyukan Shaforon da Kodumti dake karamar hukumar Numan, jihar Adamawa.
Kamar yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Suleiman Nguroje, ya shaida wa manema labarai cewa ana zargin fulani makiyaya ne suka kai wannan harin.
” Yanzu dai wadanda aka kashe suna dakin ajiye kawa a asibitin Numan, sannan wadanda suka ji ciwo suna asibiti ana duba su. Zuwa yanzu an kara tura jami’an tsaro domin farautar wadanda suka far wa kauyukan.”
Wani mazaunin kauyen Lawrence Shinkoko, yace maharan sun farwa kauyen da yawansu ne da misalin Karfe daya na dare, sannan suka rika bude wuta babu kakkautawa.