Mahara sun farwa garin Takum, sun kashe mutane da dama

0

Wasu mahara dauke da bindigogi sun farwa garin Takum dake jihar Taraba inda suka kashe mutane da dama a wannan harin.

Mazauna wannan gari sun bayyana cewa lallai wadannan mahara ‘yan kabilar Tiv ne daga jihar Benuwai. Sun farwa garin Takum din ne domin daukar fansar wani nasu da aka kashe.

Maharan sun biyo ta tsaunikan Angwan Abakwa dake kusa da garin Wukari.

Mazauna garin sun ce wannan hari na da nasaba da kisan da aka yi wa wani limamin coci David Tanko da aka yi a wannan gari a daidai yana dawowa daga wani ganawar sulhu da ya je tsakanin ‘yan kabilar Tiv da Jukum da rikici a tsakanin su ya ki ci yaki cinyewa.

A cewarsu wannan kisa da akayi wa fasto David ne ya tunzura ‘yan Kabilar Tiv su dau fansa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Taraba, David Misal ya bayyana cewa wasu ne dauke da bindigogi suka diran wa garin suna bude wuta ta ko ina inda suka kashe mutane.

Misal ya ce ‘yan sanda zasu bayyana yawan wadanda aka kashe da wasanda suka samu rauni bayan sun gama bincike.

Share.

game da Author