Sama da malaman firamare da na karamar firamare 7000 ne ke neman hakkin ariyas din albashin sun a watanni daga 8 zuwa 39 daga hannun Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.
Wadannan malamai sun yi wannan kiran a biya su hakkin na su ne a wani taron gaggawa da suka gudanar na Kunyiyar Malamai ta BASAN a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Sun gudanar da wannan game-garin taron ne a jiya Litinin.
Kungiyar ta bayyana cewa sun shiga wannan tsomomuwa da katankana tun cikin 2016, lokacin da da gwamnatin jihar ta bijiro da tsarin tantance malamai.
Sun kara da cewa malaman da wannan rashin biya kudin ariyas na albashin tsawon lokaci ya shafa, duk sun koma mabarata, saboda kiciniyar neman ciyar da kai da kuma iyalan su.
Sanarwar ta ce wannan jinkirinya shafi malamai 7000 daga cikin 23,000 da ke karkashin kungiyar ta su a fadin jihar.
Shugaban Riko, Onotu Yahaya da Sakataren kungiya, Mohammed Sule ne suka sanya wa takardar bayan taron da ta fitar da wadannan bayanai hannu, bayan kammala taro.
Sannan kuma sun nuna takaicin yadda aka kasa biyan karin mafi kankantar albashi na naira 18,000.
Ya ce amma malaman babbar sakandare tun 2011 ake biyan su tsarin naira 18,000 mafi kankantar albashi.
“Sannan kuma da yawan malaman firamare da na karamar sakandaren da suka yi ritaya, sun kasa fara samun kudaden fanshon sun a kowane wata. Duk ba a fara biyan su ba, ballatana maganar garatuti kuma.’
Bayan sun ci gaba da nuna damuwar su dangane da yadda aka tauye musu hakkin su, sun kara yin kira da a gaggauta biyan su ba tare a wani bata lokaci ba.
Discussion about this post