Idan ba a manta tun a 2015 ne wato alokacin da ake gwagwarmayar Kamfen da neman takara gwamna El-Rufai ya bayyana cewa idan yayi nasara zai saka dansa a makarantar gwamnati.
Tun a wancan lokaci ana ta ganin El-Rufai ya fada ne kawai amma bazai iya haka ba saboda lalacewar makarantun gwamnatin jihar.
Wannan cece-kuce dai an gama shi daga yau litini 23 ga watan Satumba, domin kuwa gwamna El-Rufai ya ba mara da kunya, ya garzaya da dan sa Abubakar ma shekaru 6 zuwa makarantar gwamnati na Capital School in da aka yi masa rajistan shiga aji daya.
El-Rufai ya bayyana haka a shafinsa na tiwita inda yayi kira ga sauran jami’an gwamnati da su koyi da shi su saka ya’yan su a makarantun gwamnati kamar yadda yayi.
Mutane da suka tofa albarkacin bakinsu game da wannan abu da gwamna El-Rufai yayi sun jinjina masa sannan sun yi kira ga sauran gwamnoni da jami’an gwamnati da su yi koyi da El-Rufai.
” Wannan abu da gwamna El-Rufai yayi ya tabbatar mana cewa El-Rufai mutum ne mai cika alkawari. A lokacin da ya fadi cewa zai saka dansa a makaranta mutane da dama sun karyata haka. yau dai yar fara ta nuna ya cika alkawarin da ya dauka.” Inji Hassan Lawal
Tun bayan darewa gwamna El-Rufai kujerar mulkin Kaduna ya fara aiki tukuru wajen gyara makarantun firamaren jihar. Zuwa yanzu dai kusan makarantun jihar sun kusa kammaluwa da gyara da kuma sabbin gine-gine.
An samu karin dalibai da kuma daukan malamai kwararru da yayi.