Wata kotun cikin gida ta hukumar tsaron sojoji da aka kafa, ta fara binciken Manjo Janar Hakeem Otiki. An kafa kotun ce a kebance a Abuja, kuma ta fara zaman ta jiya Talata.
Masu kare Otiki na kokarin nuna cewa ‘yar-tsama da tseren neman mukamin da ke tsakanin Janar Otiki da Laftanar Janar Lamidi Adeosun na daga cikin dalilin da su ke ganin bai kamata Adeosun ya zama shi ne shugaban kotun hukunta Otiki ba.
Duk da cewa masu kare Otiki ba su bayyana dalilan ’yar-tsamar da ke tsakanin wadannan manyan sojoji biyu ba, amma dai wani babban jami’in soja da ke da kusanci da su biyun ya ce rajin jituwar ta su ta samo asali ne daga kutinguilar wanda zai gaji Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, wanda shi ma Laftanar Janar ne.
Hakeem Otiki da ake tuhuma daga jiya Talata dai shi ne babban jami’in sojan da ake zargi an yi wa safarar zunzurutun kudi a cikin watan Yuli, daga Sokoto da niyyar kai su Abuja, amma kuma bayan an yada zango a Kaduna, sai sata ta saci sata.
Shi ne babban kwamandan Rundunar Sojoji ta 8 da ke Sokoto.
‘ Sata Ta Saci Sata’
PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo musu labarin mai cike da abin kunya, inda wasu kananan sojojin da aka damka wa kudin su yi rakiyar su, su ka arce da su gaba daya.
Rahotanni sun bayyana cewa kudin sun kai naira milyan 800, yayin da wasu rahotannin kuma suka ce naira milyan 600 ne. Akwai kuma wadanda suka ruwaito cewa naira milyan 400 ne kudin.
Bayan sojojin sun arce da kudin, har yanzu shiru ka ke ji kuma har yau babu labarin kama su ko kuma yadda suka yi da kudin.
Bayan sojojin sun dibga wa Hakeem Otiki wannan sata, hukumar tsaro ta sojoji ta damke shi, inda aka yi masa daurin-talala a gida, aka tsare shi ba tare da ko da lekowa kofar gida ba. Daga nan an ritsa shi inda sojoji suka yi masa tambayoyin kwakwaf.
Daga nan kuma a jiya Talata ne kotun hukunta sojoji ta fara zaman ta a cikin ‘Officers’ Mess’ da ke Asokoro, Abuja.
Janar Otiki a Kotu, Kan Keken Guragu
An gabatar da Manjo Janar Otiki a kotun a kan keken guragu, kamar yadda ake ganin hoton sa a wannan labarin. Lauyan sa ya bayyana wa sojojin da ke shari’ar cewa wanda ya ke karewa, wato Otiki ba shi da cikakkar lafiya.
Mambobin Kotun Hukunta Otiki
An nada Laftanar Janar Adeosun matsayin shugaban kotun. Sauran mambobin sun hada da Manjo Janar A. Tarfa, Manjo Janar F.O Agbugor, Manjo Janar F.A Nadu, Manjo Janar N. Mohammed, Manjo Janar C.T Olukotu da kuma Manjo Janar C.C Okonkwo.
Karaji Da Gardandami a cikin Kotun
Sai dai kuma yayin da Laftanar Janar Janar Adeosun ya bude zaman kotu, sannan ya yi tambayar cewa shin ko duk an amince da wadannan mambobi na kotun hukunta Hakeem Otiki, a nan ne kallo ya koma sama,
Nan da nan sai Majo Janar Femi Oyebanjo Mai Ritaya, kuma daya daga cikin lauyoyin da ke kare Manjo Janar Hakeem Otiki, ya bayyana cewa, shikenan ai wanda ya ke karewa ya shiga ruguguwar matsala kenan, domin akwai jikakka da ‘yar-tsama tsakanin sa da shi shugaban kotun, Laftanar Janar Adeosun.
Daga nan sai ya fara irin karajin su na lauya cewa wanda ya ke karewa din ba zai samu adalci a kotun ba, saboda ‘yar-tsamar da ke tsakanin su. Haka ita ma jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Trust ita ma ta tura wakili a kotun domin halartar sauraren shari’ar tare da wasu wakilan jaridu.
Amma kuma an ce dukkan ’yan jaridar su fice, yayin da hayaniya da gardandami suka harde a kotun.
‘KA NA NUKURA DA OTIKI’ – Lauya
“ Mu na da shaida da hujja cewa ka na nukura da wanda na ke karewa.” Haka aka ruwaito lauya kuma tsohon Janar na soja, Oyebanjo ya shaida wa Shugaban Kotu.
Mai Ritaya Oyebanjo, wanda ya na daya daga cikin lauyoyin da ke kare Otiki, ya taba rike Sashen Tsare-tsaren Al’amurran Sojoji kafin ritayar sa.
“Dalilin mu kuwa shi ne: a fili ta ke cewa Janar Otiki ya shiga NDA a ranar 10 Ga Janairu, 1983, yayin da kai kuma kashiga a ranar 4 Ga Yuli, 1983. Don haka ya riga ka shiga. Kowa ya san cewa Janar Otiki ya raine ka a cikin sojoji, kuma ya ba ka horo, wato ya yi tirenin din ka.” Inji Oyebanjo.
“Don haka mu na jin har yanzu ka na kullace da shi. Sannan kuma Janar Otiki ne ya karbi shugabancin Kwamandan Zaratan Sojojin Kasa (Infantry) daga hannun ka.
Tonon Silili a Kotu
“To mu na da sane da cewa tun daga ranar da aka kara maka girma zuwa Laftanar Janar, ya aika maka da sakon tes na taya ka murna, amma saboda ka na nukurar da shi, har yau ba ka maida masa amsa ba.
“Ranka ya dade bari ma ka kara jin wata sabuwa. Ai matsawar ma idan aka fara wannan shari’a ka’in-da-na’in, wasu batutuwa za su fito fili, wadanda sun shafi ofishin ka a lokacin da ke Shugaban Gudanar da Tsare-tsaren Yakin Sojoji. Wannan mukamin ne ka bari zuwa wanda a halin yanzu ka ke a kai.
“Yallabai a nan ina magana cewa Janar Otiki ya yi Shugaban GOC ta 8 inda ya gudanar da ‘Operation Sharan Daji’ da kuma ‘Operation Harbin Kunawa III.”
Daga nan sai lauya Oyebanjo ya kara da cewa, dukkan wadannan ayyuka an yi su ne a karkashin bangaren ka. Sannan kuma wadannan batutuwa duk za su taso acikin wannan shari’a. Don haka kai ma ka na ciki tsundum kenan.”
” Da Goyon Bayan Ka Sojoji Biyar Suka Sace Kudin” – Inji Lauya
Lauya Oyebanjo ya kara yin ikirarin cewa da sanin shugaban kotunwato Janar Adeosun da kuma goyon bayan sa aka wadancan sojoji biyar suka sace kudin.
“Daga karshe ina sanar da kai cewa a lokacin da Janar Otikin ya karbi ragamar shugabancin sojojin ‘Infantry’, ya kuma gaji dukkan sojojin da ke tsaron lafiyar ka, wadanda yaran ka ne, kuma su ne suka zama jami’an tsaron shi Otiki din.”
“Wadannan jami’an tsaro ne suka haifar mana da dalilin da ya sa mu ke a nan a halin yanzu. Maganar gaskiya (wadanda suka saci kudin) sojojin ka ne, hadiman ka ne. Daga hannun ka ya gaje su. Su ne kuma suka kuntika abin da ya yi sanadiyyar zaman mu a wannan kotun a yau.
“ Ran Mai Shari’a ya dade, da wadannan dalilai ne na ke cewa kai ma ka na cikin wannan shari’a tsamo-tsamo. Idan mu na magana za mu rika yanko wata rawa da ka taka da kuma karanto sunayen ka a wurare da dama. Kenan idan za ka zama shugaban wannan kotu, to ka sani sunan ka zai rika fitowa a cikin bayanai da batutuwan da za mu rika gabatarwa a gaban ka.
“ Yallabai da wannan dalili ne na ke cewa ya kamata ka sauka daga shugabancin wannan kotu kawai.”
Ba a tabbatar ba ko shugaban kotun ya maida raddin amsa wadannan zarge-garge da aka yi masa.
Kakakin Hukumar Tsaro na Sojoji ya ki daukar wayar da Premium Times ta yi masa domin jin ta bakin sa.
Sannan kuma ba a san ranar da aka aza domin ci gaba da sauraren shari’ar ba.