Kudaden kula da tsaron jihohi sun hada Buratai da gwamnoni dambe

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya ci wa gwamnonin Najeriya kwala, inda ya kalubalanci halascin kudaden tsaro jihohin da gwamnatin tarayya ke dumbuza musu a duk kowane wata.

Kudaden da aka fi sani da suna ‘security votes’, Buratai ya ce wasu gwamnoni na fakewa da sulken kariya daga tuhuma su na ragargazar kudaden son ran su.

Sai dai kuma Gwamnan Jihar Ekiti, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa babban abin da ake bukata dai dangane da wadannan kudade a wajen kowane gwamna, shi ne ya yi amfani da kudaden yadda ya dace.

Amma kuma Buratai cewa ya yi gwamnoni na amfani da wadannan kudade ta wata hanya daban, sai ka ce ba an ba su kudaden ba ne domin dakile matsalar tsaro da kara inganta harkokin sa-ido da lura da ayyuka a cikin kasar jihohin su.

Buratai ya yi wannan bayani a wani taron tattaunawa kan muhimmancin sa-ido kan kudaden tsaron da ake bai wa gwamnoni, wanda aka gudanar a hedikwatar ICPC a Abuja.

Cikin wadanda suka halarci taron har da Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamakko da sauran manyan baki da dama.

‘Haramtattaun Kudade Ne’

Buratai ya kafa hujja da wani fitaccen lauya, Robert Clark ya yi, wanda ya ce wadannan kudaden tsaro da ake bai wa gwamnoni, haramtattun kudade na, domin babu inda doka ta amince a rika ba su kudaden a duk wata.

Ya ce gwamnoni da dama na amfani da kariya ko rigar sulken hana kama su ko binciken su a lokacin da su na mulki, su rika tabargaza da bushasha da kudaden.

An dai fara bai wa gwamnoni wadannan kudade ne a lokacin mulkin Ibrahim Babangida.

Akasari zunzurutun kudaden ne ake loda ana kai wa kowane gwamna, kuma babu wata dokar da ke bibiyar me aka yi da kudaden, ballantana hukumar bincike ko bin-diddigin kashe kudade ta bi sawun yadda kowane gwamna ya kashe kudaden.

Ana bai wa kowane gwamna kudaden duk wata da nufin ya kula da matsalar tsaron da ke addabar jihar, idan akwai matsalar ko babu.

Ana raba wa gwamnoni bilyoyin kudade duk wata, kuma ya danganta ga irin kalubalen da kowace jiha ke fuskanta.

Rahoton Kungiyar ‘Transparency International’ na 2018 da kungiyar ta yi a kan kudaden ‘yar-burum-burum, ta ce akalla kowane wata Najeriya na kashe naira bilyan 280 a kan batun ‘kudaden kula da tsaro’.

A kan haka sai Buratai ya ce ya kamata a fara bibiya da kuma rika binciken yadda ake kashe wadannan kudade, domin a tabbatar da ana yin komai dalla-dalla.

Buratai ya yanko wani bayani da Robert Clark ya yi inda ya ce: “A yi la’akari da cewa wadannan kudade fa ba kudaden aikin kare kasa ba ne da ake bai wa sojoji. Da dadewa ana raba wadannan makudan kudade ba bisa ka’idar dokar kasa ba.”

Shi kuwa Gwamna Fayemi, ya sake yin tsinkayen cewa bai kamata a fito a haramta kudaden ba, idan aka yi la’akari da kalubalen da yawancin gwamnoni ke fuskanta a jihohin su.

Sai ya ce kamata ya yi a yi nazarin irin yadda gwamnonin wasu kasashe ke amfani da irin wadannan kudade.

Share.

game da Author