Kotu ta yi fatali da kalubalantar zaben El-Rufai da PDP ta ke yi

0

Kotun sauraren Kararrakin zabe da ke zama a Kaduna ta yi fatali da kalubalantar zaben gwamna mai ci Nasir El-Rufai da jam’iyyar APC da dan takarar gwamna na PDP Isah Ashiru da jam’iyyar sa suka shigar a gabanta.

Alkalin kotun Ibrahim Bako ya bayyana cewa PDP da dan takarar ta basu bayyana hujjojin da ya gamsar da kotu ba cewa wai ba ayi adalci a wannan zabe ba da har suke bukatar a kwace kujerar gwamnan jihar a mika musu.

Ya ce gaba daya hujjojin su basu yi tasiri a gaban wannan kotu ba.

Lauyan gwamna El-Rufai Abdulhakeem Mustapha, ya yaba wa kotun inda ya ce wannan hukunci yayi daidai kuma shine yafi dacewa.

Shugaban jam’iyyar PDP Hassan Hyet ya bayyana cewa bai ji dadin wannan hukunci ba amma kuma zasu gana da sauran ‘ya’yan jam’iyyar domin fitar da matsayar jam’iyyar game da hukuncin kotun.

Share.

game da Author