Kotu ta ce gwamnati ta saki Sowore

0

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta bada umarnin gwamnatin tarayya ta saki mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore da ke tsare.

Kotun ta bayar da wannan umarni ne a yau Talata, tare da cewa babu wani sauran umarni daga wata kotu da ta ce a ci gaba da tsare shi.

Kotun ta ce amma Sowore ya kai wa kotun ajiyar fasfo din sa a cikin sa’o’i 48 bayan sakin sa.

Sannan kuma ta nemi lauyan sa, Femi Falana ya zama shi ne zai rika kawo shi kotu, da zarar an sanar da shi caje-cajen da ake yi masa.

Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya ce doka ta bai wa kowane dan Najeriya ‘yanci komai matsayin sa a sama ko rashin matsayin sa a kasa. Kuma komai arzikin sa komai talaucin sa.

“Umarnin da kotu ta bayar na ci gaba da tsare shi ya wuce. Tunda babu wata kotun da ta kara sabunta umarnin ci gaba da tsare shi, don haka wa’adin umarni na farko ya cika, ya kare. Sai a sake shi kawai.”

“Kowane dan Najeriya na da ‘yancin da kokar kasa ta ba shi, ko mai arziki ko matalauci. Mai mulki ko talaka. Danagane da haka ne na ke ganin dacewar sakin sa, ba tare da bata lokaci ba.” Inji Mai Shari’a Taiwo.

Tun a ranar 3 Ga Agusta aka kama Sowore saboda zargin zai hada gangamin zanga-zanga a fadin kasar nan, mai suna #RevolutionNow.

An yi ta sukar caje-cajen da aka ce an yi wa Sowore, ciki har da sukar Shugaba Muhammadu Buhari.

Sowore na a sahun gaba wajen goyon bayan hawan mulkin Buhari a lokacin kamfen din 2015.

Jaridar sa ta yi kaurin suna wajen sukar tsohon shugaba Goodluck Jonathan, tare kuma da nuna goyon baya ga Buhari.

Share.

game da Author