Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Simon Achuba, ya maka Gwamna Yahaya Bello Kotu. Tare da gwamnan kuma ya hada har da Kwamishinan Shari’a na jihar duk ya maka su kotu.
Achuba ya kai su kara ne saboda neman a biya shi hakkin sa na alawus-alawus da ya ce gwamnan ya ki ba shi.
A cikin takardar kara mai lamba NICN/ABJ/244/2019 da aka shigar tun a ranar 19 Ga Agusta, Achuba ya rokli kotu cewa hana shi alawus din da gwamna Bello ya yi na tsawon lokaci, nuna bambanci ne, kuma rashin adalci ne.
Sannan kuma ya nemi kotu ta sa a biya shi naira milyan 921.5 a matsayin wasu kudaden sa na alawus din tafiye-tafiye da gwamnan ya ki ba shi.
Sannan akwai wasu alawus na mako-mako, kudaden gudanar da tsaro a matsayin sa Mataimakin Gwamna da su ma suka wajaba a rika ba shi, amma duk ba a ba shi.
Ofishin sanannen lauya Falana&Falana ne ya shigar da karar a madadin Mataimakin Gwamnan na Kogi.
Dangantakar siyasa ko ta aiki tare duk ta yi tsami tsakanin Gwamna Yahaya Bello da Mataimakin sa Simon Achuba, har abin ya fito fili a cikin watan Oktoba na shekarar 2018.
Cikin watan Fabrairu, 2019, Achuba ya ce rayuwar sa na cikin hatsari, domin gwamna ya sa an janye jami’an tsaron da ke kare lafiyar sa.
Cikin watan Agusta kuma Majalisar Jihar Kogi ta fara wani yunkuri na tsige Achuba.
NAN ta ruwaito cewa akwai alamun za a ci gaba da sauraren karar, domin ayyuka sun dawo ka’in-da-na’in yau Litinin a kotun, bayan hutun watanni biyu da alkalai suka tafi.
Sannan kuma an ga lauyoyi da kuma masu shigar da kara yau Litinin a kotun.
Da alamu dai ziyarar da Mataimakin Gwamnan ya kai Fadar Shugaba Muhammadu Buhari dangane da sabanin da ke tsakanin sa da Gwamna Yahaya Bello, ba ta yi wani tasiri ba.
Karar da mataimakin Bello ya shigar a kotu na nuni da cewa Buhari ko Fadar Shugaban Kasa ko uwar jam’iyyar APC sun kasa sasanta Achuba da Bello.