Kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta inganta yin bincike a fannin kiwon lafiya a kasar nan.
Jami’a a hukumar hana yaduwar cututtuka na kasar Amurka Bolu Omotayo ce ta yi wannan kira a taron ma’aikatan kiwon lafiya da aka yi a Abuja a cikin wannan mako.
Omotayo ta ce gwamnati za ta inganta aiyukkan wadannan ma’aikata ta hanyar karo ma’aikata a fannin tare da gina makarantu domin koyar da ayyukan asibiti da kula da maradsa lafiya.
“Sanin kowa ne cewa wadannan ma’aikata ne ke gudanar da bincike a duk lokacin da cuta ko kuma cututtuka suka bullo a kasa sannan sakamakon binciken su ne ke taimaka wa gwamnati wajen hana yaduwar cututtuka a kasa.
“ Rashin samar da isassu da kwararrun ma’aikata irin haka na gurguntar da aiyukkan fannin kiwon lafiya musamman kiwon lafiyar mutanen kasar nan.
“ A dalilin haka ya zama dole gwamnati ta yi wa wannan bangare na kiwon lafiya tanadi domin kare kiwon lafiyar mutane a kasa.
Bayan haka shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’iab yace lokaci ya yi da gwamnati za ta daina shigo da siyasa a cikin harkokin kiwon lafiya.
Discussion about this post