Rahotanni daga kasar Afrika Ta kudu sun nuna cewa akalla mutum daya ne ya rasa ransa inda wasu da dama suka jikkita a zanga-zangar kin jinin baki da aka yi a kasar ranar Lahadi.
Dubban ‘yan kasar Afrika Ta Kudu sun fito a manyan titunan Johannesburg ranar Lahadi domin matsa wa mahukuntan kasar su gaggauta koran baki a kasar.
Masu zanga-zangan sun afkawa shagunan baki wadanda ba ‘yan kasan bane suka yi warwason kayan shagunan sannan kuma har da lakadawa wasu dukan tsiya.
Wannan zanga-zanga ya dawowa gwamnatin kasar da hannun agogo baya bisa kokarin da take yi na kwantar wa mutanenta hankali da rokonsu rabu da baki wadanda ba ‘yan kasan ba su ci gaba da zama da kuma yin sana’o’in su babu takura.
‘Yan sandan kasar sun ce sun yi gaggawan tattare masu zanga-zangar daga fadawa shagunan baki sannan sun yi kame da da yawa.
Idan ba a manta ba a makon jiya ne kasashen Afrika suka dau zafi a dalilin yadda ‘yan kasar Afrika Ta Kudu suke afkawa baki da cin zarafinsu wai sun amshe musu ayyukan da ya kamata ace sune suke yi amma baki sun shigo musu kasa sunayi.
A Najeriya, matasa sun fusata inda suka ciccinnawa wasu ofisoshin MTN wuta a wasu jihohi sannan kuma da farwa babban kantin Shoprite dake Legas inda suka yi wa katafaren kantin karkaf
A kasar Zambia da Congo ma an samu rahoton cewa an cinna wa ofishin jakadancin kasar Afrika Ta Kudu da ke kasashen wuta.
Shugaban Kasar Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi kira ga mutanen kasar da su janye daga farwa ‘yan wasu kasa da ke kasar sannan ya umarci ‘yan sanda su cafke duk wanda yayi wa umarnin kunnen uwar shegu.