KEBBI: Kungiyar Kwadago ta yi fatali da fara biyan naira 30,000 mafi kankantar albashi

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa Reshen Jihar Kebbi, ta yi fatali da kuma nuna rashin yarda da fara shirin biyan naira 30,000 mafi kankantar albashi da gwamnatin jihar ta yi sanarwa za ta fara daga karshen wannan wata na Satumba.

Shugaban Kungiyar na Jihar Kebbi, Umar Halidu ne ya bayyana wa manema labarai haka, yau Labara, bayan tashin da suka yi daga wani taron gaggawa.

Halidu ya ce sun ki yarda da fara biyan sabon albashin ne bayan taron da suka gudanar tare da wakilan mambobin sun a dukkan kananan hukumomin jihar 21.

Ya ce gwamnatin jihar Kebbi ba ta tuntube su ba, domin jin adadin kudaden da aka kara wa masu matakin albashi daga na 07 zuwa sama.

Ya ce ita dai gwamnatin tarayya abin da ya ce shi ne za a maida mafi kankantar albashi daga naira 18,000 zuwa 30,000. Kuma masu wannan adadi kananan ma’aikata ne masu masu matakin albashi daga na 01 zuwa na 06.

Ya nuna mamakin yadda gwamnatin jihar ba ta tuntubi kungiyar kwadago ba domin zaman tattauna abin da za a kara wa masu matakin albashi daga na 07 zuwa sama.

Halidu ya ce gwamnatin Kebbi ita kadai ta yi kidan ta, kuma ta yi rawar ta. Don haka ba za su yarda ko amince da duk wani ‘yar burum-burum da za a yi wa ma’aikatan jihar ba.

A kan haka ne ya ce ba su amince da tsarin karin da aka shigo da shi ba, domin ba a yi shawarar da su kamar yadda ya kamata a yi ba, domin tattauna abin da za a kara wa masu matakin albashi na 07 zuwa sama ba.

Daga nan ya yi kira ga dukkan mambobin kungiyar na jiha baki daya da su kwantar da hankalin su, domin kungiyar su ta kwadago na nan na kokarin ganin tabbatacin sun kwato wa dukkan ma’aikatan jihar hakkokin su.

Share.

game da Author