Katsinawa, Sakkwatawa da Zamfarawa 40,000 ke gudun hijira a Nijar -UN

0

Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), ta bayyana cewa akwai ‘yan Najeriya sama da 40,000 da suka tsere gudun hijira zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

Ta ce wadannan dukkan su sun fito ne daga jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara, a Arewa maso Yamma, inda ‘yan bindiga suka hana mazauna yankin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A rahoton da suka buga ranar Juma’a, Kakakin UNHCR, Babar Bolach ya ce wadannan masu gudun hijira sun nunka a cikin watanni goma kacal. Ya ce a ciki kin watan Satumba, ranar 11 Ga Satumba, an samu karin masu gudun hijira daga Zamfara, Sokoto da Katsina har 2,500.

Daga nan ya ce UNHCR za ta hada hannu da gwamnatin Nijar domin a bada tallafi da agaji ga sabbin zuwan sannan kuma a yi musu rajista.

UNHCR har ila yau ta ce wadannan ‘yan gudun hijira wadanda yawancin su mata ne da kananan yara, su na zaune cikin kauyuka sama da 50 a Nijar.

Cikin kauyukan da aka lissafa ‘yan Najeriya ke gudun hijira, har da Gidan Runji, Gidan Sori da Tsibiri.

Abin takaici inji UNHCR, a can Nijar din ma su na fama da ‘yan bindiga a kan iyaka, masu kai musu hare-hare, har da karkashe musu dagatai da masu unguwanni.

Wadannan masu gudun hijira 40,000, da ban su ke da dubban masu gudun hijira daga Najeriya zuwa Nijar da Boko Haram suka kora a Yankin Arewa masu Gabas daga Barno da Yobe.

Share.

game da Author