KARIN ALBASHI: Har yau Gwamnati ta kasa cimma matsaya daya

0

A wani zaman da aka yi tsakanin Wakilan Gwamnatin Tarayya da na Majalisar Tattaunawar Kungiyoyin Ma’aikatan Gwamnati (JNPSNC), an kasa cimma yarjejeniya a kan yadda za a saisaita tsarin biyan karin albashi.

Babban Sakataren JNPSNC na bangaren ma’aikata, Alade Lawal, ya shaida wa manema labarai cewa Kungiyar Kwadago za su je su zauna su yi tunanin mataki na gaba da za su dauka dangane da batun karin mafi kankantar albashi. Ya ce kuma nan ba da dadewa ba za su sanar da ’yan Najeriya halin da ake ciki.

“Mun yi taro don taro kam, amma an tashi baram-baram. Saboda mun gano cewa wakilan da da Gwamnatin Tarayya ta turo domin tattauna cimma yarjejeniya da mu, ba da gaske suke yi ba. Sun maida batun karin albashin abin wasa kawai. Mu na zargin akwai makarkashiya ko kuma rainin wayo a batun gaba daya.

“Mun yanke shawarar mika rahoton abin da ya faru a wurin taron ga shugabannin mu, ciki kuwa har da Shugabannin Kungiyoyin Kwadago. Daga nan za a sanar wa ’yan Najeriya matakin da za mu dauka a gaba, nan ba da dadewa ba.”

Shugaban tawagar kungiyar kwadagon da suka halarci taron, Simon Anchaver, ya ce za su aika dukkan gamayyar kungoyoyin kwadago da kungiyoyin ma’aikatan gwamnati da shawarar matakin da ake ganin shi ya kamata a dauka.

Daga nan sai ya ce irin yadda gwamnati ke jan-kafa da tafiayar hawainiya wajen batun karin albashi, tamkar tsokana ce suke wa kungiyoyin kwadago domin su tafi yajin aiki. Saboda ma’aikata na cikin halin takoken ko za a sakar musu dukkan kudaden ariyas din su da zaran an kammala wannan tattauna wadda mu ka zauna, amma aka yi wasarere da batun na karin albashi.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Winifred Oyo-Ita ce ta shugabanci taron, yayin da Shugaban Riko na Hukumar Saisaita Albashi da Kudaden Shiga ta Kasa ya kasance Sakataren taron a lokacin zaman tattaunawar.

Tun cikin watan Afrilu ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa dokar karin albashi hannu. Amma har yau ana ta jula-jular yadda za a fara aiki da sabon tsarin karin albashin.

An yi ta kawo kabli-da-ba’adin yadda karin albashin zai kasance a kowane matakin albashi.

Sai dai su kuma hadaddiyar kungiyar JNPSNC cewa ta yi tunda mafi kankantar albashi zai tashi daga naira 18,000 zuwa naira 30,000, wato karin kashi 66 bisa 100 na naira 30,000, don haka kowane matakin albashi ma’aikaci ya ke, tilas a kara masa kashi 66 bisa 100 na yawan albashin da ya ke dauka.

Ma’ana, mai daukar naira 180,000 ya kasance an rika biyan sa naira 300,000 ba tare da wata jikara ba.

Share.

game da Author