Sakamakon wani bincike da akayi a jami’ar Newcastle dake kasar Birtaniya ya nuna cewa karfin kwan halittan namiji ne ke sa ma’aurata su haifi da namiji ko kuma ‘ya mace.
Binciken ya nuna cewa lallai idan a zuri’ar mutum mata sun fi yawa to zai fi yawan haihuwar mata ne a cikin ya’yan sa. Haka kuma idan mazane suka fi yawa a zuri’arsu to zai fi yawan haihuwar ‘ya’ya mata ne.
Likitocin da suka gudanar da wannan bincike sun bayyana cewa sun duba tsarin wasu iyalai ne da ya kai 927 da kuma yadda taswirar haihuwarsu da na ‘ya’yan su yake da ya kunshi bayanai akalla 556,387 tun daga yanzu akayi baya har zuwa 1600.
Bayan an gudanar da wannan bincike sai aka ganowa cewa lallai ana samun yawan haihuwan ‘ya’ya maza ne idan har a zuri’ar maigida maza sun fi yawa to shima zai fi yawan haihuwar maza. Haka kuma idan ma mata ne toh mata za afi haihuwa.
” Karfin kwan hallita dake dauke a cikin maniyyin namiji shine ke sa a haifi da namiji ko kuma ‘ya mace. Idan kwan hallita X ya gamu da na mace a lokacin saduwa X to sai a haifi mace, idan kuma kwayar Y ce aka harba ta gamu da X sai a haifi namiji.
Likitocin sun ce binciken ya nuna idan har ana samun iyalai da mata ne aka haihuwa a tsarin zuri’arsu, toh mata ne za sufi ya wa, za su zarce yawan maza da sai ya zamo maza na wahala a kasar.
Discussion about this post