Hukumar Sa-ido Kan Hana Laifukan Da Suka Saba Shari’ar Musulunci (Hisbah), ta bayyana kamawa da fasa kwalaben giya 196,400 duk a cikin Kano.
Haka hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Mataimakin Gwamna, Hassan Musa-Fagge ya saw a hannu.
Da ya ke jawabi jim kadan bayan halartar wurin fashe kwalaben a dajin Kalemawa, cikin Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa addinin Musulunci ya haramta shan jiya da duk sauran wasu abubuwan sa maye da bugarwa, wadanda za su iya yi wa kwakwarwar mutum lahani.
“ Malaman mu na addinin musulunci, da shugabannin mu su hada hannu domin yaki da wannan lamari na kawar da kayan shaye-shaye masu bugarwa.” Inji Ganduje.
Ganduje na magana ne ta bakin Mataimakin Gwamna, Nasiru Gawuna, wanda shi ne ya wakilce shi.
Ya tabbatar da cewa dukkan sauran hukumomin jihar za su samu goyon baya irin daidai da irin wanda gwamnatin jihar ke bai wa Hisbah, domin gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.
Da ya ke jawabi, Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Haroon Ibn-Sina, ya ce hukumar ta samu nasarar hana tu’ammali da barasa a karkashin dokar Shari’a ta 401 ta Penal Code ta 2013.
Ya ce Hisbah ta nemin umarni daga kotu, kuma ta samu na farfasa kwalaben giya har lodin motoci 12.