Kamfanin Sadarwa na MTN ya sanar da rufe duke ofisoshinta na hulda da jama’a dake fadin kasarnan har sai komai ya lafa.
Idan ba’a manta ba tun a ranar Talata ne ‘yan Najeriya suka harzuka domin daukan fansa akan cin zarafin ‘yan Najeriya da ake yi a kasar Afrika ta Kudu saboda wai don ba ‘yan kasa bane.
Wannan cin mutunci bai tsaya ga ‘yan Najeriya ba kawai, har da sauran ‘yan wasu kasashen duniya basu tsira ba daga hare-haren su.
Sukan shiga shagunan wadanda ba ‘yan kasa ba suna farfasa kayan ciki sannan su saci na sata da sunan wai sune suka hana su aikin yi.
Abi ya kai makura, inda a ranar Talata matasan Najeriya cikin fushi tunkari shagona, wanda mallakin ‘Yan Kasar Afrika Ta Kudu ne suna ciccina musu wata.
A jihar AKwa-Ibom, an cinna wa ofishin MTN wuta sannan a Jihar Legas da Ibadan, a farwa shagunan Shoprite wanda mallakin ‘yan asalin Afrika Ta kudu aka yi masa karkaf.
Yanzu MTN ta sanar cewa ba za ta bude ofisoshinta ba har sai komai ya lafa.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi tir da wannan aika-aika da cin zarafin ‘yan Najeriya da ake yi a Kasar Afrika Ta Kudu sannan tuni ya yi wa Jakadan Najeriya a Kasar kiranyen gaggawa da kuma janyewa daga halarta taron da za a yi na kasa da kasa a kasar.
Mataimkin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci tawagar Najeriya a wannan taro.
Bayan haka, shugaba Buhari ya umarci kasar Afrika Ta kudu da ta biya diyyar dukiyar da ‘yan Najeriya