A ranar alhamis 12/09/2019, wata kotu a birnin Kano ta bayar da belin shahararren mawakin hausan nan, wato Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Naziru Sarkin Waka.
Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta gurfanar da shahararren mawakin a gaban kuliya bayan kama shi ranar Laraba.
Wai suna tuhumar Naziru ne akan wasu wakoki da yayi yau kusan shekaru hudu da suka gabata.
Wakokin sun hada da ‘Gidan Sarauta’ da ‘Sai Hakuri.’
An kama mawakin, wanda shine Sarkin waka na Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ranar Laraba da yamma.
A ranar Alhamis kotun ta bayar da belin sa bisa sharadin cewa zai bayar da fasfo dinsa da kuma samar da mutanen da za su tsaya masa.
Muna rokon Allah, don tsarkin sunayen sa, don so da kaunar da muke yiwa Manzon sa (SAW), yayi muna maganin wadannan azzalumai, amin.
Sannan muna kira ga dukkan ‘yan Najeriya, da Kanawa, da dukkan masoyan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi, da suyi hakuri, kar su damu, da yardar Allah mu muna sane da cewa, karshen azzalumi jin kunya; sannan shi zalunci ba zai taba dore wa ba. Sannan da yardar Allah, wadannan mutane za su yi tsiyar su su gama, amma wallahi, da karfin ikon Allah, ba za su taba yin nasara akan Mai Martaba Sarki ba!
Sannan duk wani sharri, makirci, da kulle-kullen su, zai koma masu da yardar Allah!! Sai sun yi dana-sanin duk abinda suke yi da yardar Allah!!!
Ina rokon Allah da yaci gaba da kare muna Mai Martaba da mutuncin sa, don alfarmar Manzon Allah (SAW), amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau