KAFA KWAMITIN MASHAWARTA KAN TATTALIN ARZIKI: Sarki Sanusi ya yaba wa Buhari

0

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari dangane da kwararrun masana harkokin tattalin arzikin da ya zabo ya nada a matsayin mashawartan sa a kan tattalin arziki.

Sarkin Sanusi ya ce Buhari bai yi zaben-tumun-dare ba, domin ya zabo kwararru kuma wadanda suka karanci fannonin tattalin arziki daban-daban.

Sarkin Kano ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a fadar sa, a Kano.

Sarki Sanusi II ya bayyana wannan majalisar mashawarta tattalin arziki da Buhari ya nada a matsayin kwararru, kuma ya kara da cewa nada su ya zo daidai lokacin da ake matukar shawarwarin irin su domin kudirin Buhari na kara bunkasa tattalin arziki.

Ya ce ‘yan Najeriya na cike da muradin ganin sun karu da irin dimbin ilmin da wadannan kwararrun masana tattalin arziki da Buhari ya nada domin ba shi shawara a fannin bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sarki ya ce kuwa wani abin sha’awa da wannan majalisar mashawarta shi ne irin dimbin gogewar da gare su a harkokin tattalin arziki a fannonin harkokin zaman kan su.

“Idan ku ka dubi irin tsarin gwamnatin da gare mu, kuma ku ka dubi irin tsarin ta Amurka, to za ku ga duk wani shugaban da aka yi a Amurka ya na da mashawarta kan fannin tattalin arziki.

“Abi da shugaban kasa ya yi shi ne ya bi tsarin kafa majalisar kwamiti da zai rika ba shi shawara a kan hanyoyin bunkasa tattalin arziki a wannan mawuyacin halin da kasa ke ciki.

‎Sanusi II ya ce dama idan tattalin arzikin duniya ya shiga irin wannan halin, to akwai bukatar shugaban kasa ya kafa majalisar masu ba shi shawara a kan hanyoyin bunkasa tattalin arziki.

Sarki Sanusi II dai ya yi shugabancin babban bankin Najeriya, CBN kafin ya zama Sarkin Kano.

Share.

game da Author